...An Kashe Biyu Daga Cikin Masu Garkuwan
Rundunar Sojojin Nijeriya, ta 33, dake Bauchi, ta ceto wani saurayi Muhammad Musa, mai shekaru goma sha shida da haihuwa a hannun masu satar mutane a kauyen Rafin Gigidake karamar hukumar Akaleri, a jihar Bauchi.
Shi dai wannan matashi ranar juma’ar data gabata ne aka sace shi, amma sai da aka kai ruwa rana tsakanin Sojoji da wadanda suka sace yaron.
Kwamadan Sojojin kaftin Harrison Chigozie, a lokacin da yake gabatar da yaro da manema labarai, yace a kokorin ceto yaron bayan masu satar mutane suka karbi kudin Naira dubu dari bakwai da saba’in sun kashe mutane biyu a cikin wadanda suka sace yaron kuma sun kwaso kudaden da suka amsa ba fansa.
Kawun yaro mai suna Ali Umar, cewa yayi tun daka sace yaron dashi suke Magana kuma abinda suka nema shine miliyan daya da dubu dari shida amma dubu dari bakwai da saba’in aka samu ko suma rance ne.