Tsohon Gwamnan Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana dalilin rashin halartar bikin cikar Sarkin Musulmi 10 kan sarauta inda ya nuna cewa masarautar ba ta ba shi goron gayyata ba.
Ya ce, a matsayinsa na Garkuwan Sokoto kuma wanda shi kadai ya tsaya wa Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Saad II aka ba shi sarautar amma kuma masarautar ba ta mutunta ta shi ba.
Bafarawa ya yi zargin cewa wadanda suka shirya bikin ne suka kulla wannan makarkashiya na kin bashi wani rawa da zai taka a yayin bikin yana mai cewa ya kauracewa taron ne don gudun aukuwar wani abin Jin kunya.
Title :
Sarkin Musulmi Bai Gayyace Ni Bikin Cikarsa Shekara 10 Kan Sarauta Ba - Bafarawa
Description : Tsohon Gwamnan Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana dalilin rashin halartar bikin cikar Sarkin Musulmi 10 kan sarauta inda ya nuna c...
Rating :
5