Rundunar 'Yan sanda Ta Girke Manyan Makamai
A yayin da ake shirye shiryen gudanar da zaben kujerar Gwamnan jihar Ondo a yau Asabat, rundunar 'yan sanda ta girke manyan motocin yaki masu sulke guda 22, kananan jiragen yaki na ruwa guda 20 sai jirage masu saukar Angulu guda biyu ba ya ga jami'an 'yan sanda 26,000 da aka tanada da shirin ko ta-kwana.
Da yake karin haske game da matakin, Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan sanda, Joshak Habila ya ce an ba su umarnin cafke duk wani dan siyasa da aka samu yana raba kudi ga masu kada kuri'a inda ya ce ba a amince wa kowane mutum ya je rumfunar zabe da kudin da ya wuce 5000.
Title :
Rundunar 'Yan sanda Ta Girke Manyan Makamai A Jihar Ondo
Description : Rundunar 'Yan sanda Ta Girke Manyan Makamai A yayin da ake shirye shiryen gudanar da zaben kujerar Gwamnan jihar Ondo a yau Asabat, ru...
Rating :
5