----------------------------
Kamar yadda kowa ya sani musamman mazauna garin Kaduna babban masallacin Sultan Bello yana cikin halin kaka nakayi akan waye zai limanci masallata a masallacin tun bayan dakatar da Sheikh Balele Wali da akayi
Kungiyar Jama'atu da ke da iko akan masallatai da nada limamanta Wanda sarkin musulmai ke jagoranta ta nada Dr. Khalid a matsayin limamin masallacin na rikon kwarya inda Sheikh GUMI ya wasa wukarsa akan bai yarda ba.
Sheikh GUMI yace shine da masallatan wannan masallaci ke da ikon nada limamin masallacin ba kungiyar Jama'atu ba.
Sheikh GUMI Ya ce ba za su amince da nadin Jama'atu ba Wanda sarkin Zazzau ya saka ma hannu.
Ya ce abar Jama'a su zabi limamin su ba wata Jama'atu ba.
Yanzu dai ya kai ga cewa masallacin Sultan Bello na Neman ya gagari masallata domin harkusan yaki aka kusa yi tsakanin magoya bayan malaman biyu.
Gidan Jaridar Premium Times ta tattauna da GUMI da Khalid. Kuma dukkansu sun nuna cancantansu akan shugabancin masallacin.
Wadansu na zargin Sheikh GUMI da son Dora zabinsa ne a matsayin limamin masallacin inda Jama'atu ba ta bashi wannan damar ba shine yake ta kokarin ganin babu Wanda zai yi idan ba zabinsa bane.
Shi Kuma Dr. Khalid wasu na zargin sa da yin rufa-rufa da amfani da kujeransa na sakataren Jama'atu domin zama limamin masallacin.
Me za kuce akan hakan
Source premiumtimesng
Title :
Rikicin Masallacin Sultan Bello- Tsakanin Gumi Da Dr. Khalid, Waye Mai Gaskiya?
Description : ---------------------------- Kamar yadda kowa ya sani musamman mazauna garin Kaduna babban masallacin Sultan Bello yana cikin halin kaka n...
Rating :
5