*Babban Jami'in Soja Daya Da Sojoji Hudu Sun Rasa Ransu
...Yayin da aka kashe 14 daga cikin 'yan Boko Haram din
A jiya Juma'a da misalin karfe goma na dare ne wasu 'yan Boko Haram suka kai farmaki kan Bataliya ta 119 na rundunar sojojin Nijeriya dake Malam Fatoru a jihar Borno.
A yayin farmakin an kashe 'yan Boko Haram guda sha hudu, inda babban jami'in soja daya da sojoji hudu suka rasa ransu. Daya daga cikin jami'in sojan da aka kashe, har da Kanal Muhammad Abu Ali wanda shine kwamandan dakarun Task Force na 272.
Haka kuma sojojin sun kwato makamai daga wurin 'yan Boko Haram din.
Title :
Photos: Yan Boko Haram Sun Kaiwa Sojoji Farmaki
Description : *Babban Jami'in Soja Daya Da Sojoji Hudu Sun Rasa Ransu ...Yayin da aka kashe 14 daga cikin 'yan Boko Haram din A jiya Juma'a...
Rating :
5