Rahotanni daga garin Saminika dake jihar Kaduna sun nuna cewa yanzu haka wasu jami'an 'yan sandan cikin motoci uku, sun je muhallin sabuwar HUSAINIYYAH da aka gina suna rushewa.
Kamar yadda rahotanni suka nuna, ita dai wannan Husainiyyah an gina ta ne watanni biyu da suka gabata, don cigaba da gudanar da tarurrukan mabiya Shi'a a Saminaka, inda daga bisani wasu suka yi yunkurin tada rikici akan ginin, abin da ya sa Gwamnantin Kaduna ta shigar da karar yan Shi'a Kotu a Kaduna, yayin da ita kuma kotu ta dakatar da ginin wajen da kuma cigaba da yin tarurruka a wajen. Inda maganar na kotu amma sai aka wayi gari jami'an tsaro suna rushe wajen a yau.
Title :
Photos : Jami'an Tsaro Sun Rushe Sabuwar Husainiyyah Da Ake Ginawa A Saminaka
Description : Rahotanni daga garin Saminika dake jihar Kaduna sun nuna cewa yanzu haka wasu jami'an 'yan sandan cikin motoci uku, sun je muhallin...
Rating :
5