Daga Rariya
Wata tawagar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi mata izinin binciko mai a yankin Arewa Maso Gabas Karkashin hukumar NNPC ta fara aiwatar da aikin ta a jihar Bauchi. Wanda zuwa yanzu sun cimma gano yankin da za su fara gwaje-gwajen su dan soma aikin neman man fetur a jihar Bauchi.
Masanan dai sun kwashe tsawon a wanni a Dajin Kolmani dake karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi kafin su kai ga ainahin yankin da suke nema. Wanda bayan samun wannan yanki ne suka tabbatar wa duniya cewa tabbas suna da yakinin fara wannan aiki cikin nasara a wannan yanki na Arewa maso gabas.
Kafin wannan zuwa dai kwanakin baya Shugaban kamfanin man fetur na NNPP, Dakta Mai Kanti Kachalla Baru, ya kawo wata ziyara zuwa jihohin Bauchi da Gombe inda ya tabbatarwa duniya cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya umarce su da su tabbatar da an bincike man fetur din dake wannan yanki na Arewa maso gabas. Inda a lokacin Gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, ya sha alwashin goyon bayan hukumar NNPC, domun ta yi nasarar wannan aiki na tono man fetur a jihar Bauchi.
Gwamnan jihar Bauchi Barista Muhammad Abdullahi Abubakar Esq, ya yi alkawarin baiwa dukkan ma'aikatan da za su gudanar da wannan aiki na binciken danyen man fetur kyakkyawar kulawa domin wannan aiki ya yi nasara.
Ana sa ran gudanar da wannan binciken man fetur ne a wasu daga cikin kananan hukumomin jihar Bauchi da suka hada da Alkaleri, Misau da ma wasu kananan hukumomin a jihar Bauchi.
Title :
Photos: Aikin Binciken Man Fetur Ya Fara Kankama Yanzu Haka A Jihar Bauchi
Description : Daga Rariya Wata tawagar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi mata izinin binciko mai a yankin Arewa Maso Gabas Karkashin hukumar NNPC ...
Rating :
5