Ministan aikin noma, Cif Audu Ogbeh ya bayyana cewa Najeriya takusa ta fara fitar da shinkafa mai kyau zuwa kasar waje da sairan sassan duniya.
Jaridar Punch ta bada rahoton cewa ministan ya bayyana hakan ne a ranan juma’a, 11 ga watan Nuwamba a wata yawon duba gonakin shinkafa a karamar Hukumar Auyo a jihar Jigawa.
Ogbeh na tare da gwamnan babban bankin najeriya,Mr. Godwin Emefiele, gwamnan jihar kebbi,Abubakar Atiku Bagudu da Mohammed Badaru Abubakar gwamnan jihar Jigawa.
Yace: “Lokacin da muka fada ma yan najeriya cewa cikin wata 2 a wata shekara ba sanu bukaci a shigo mana da shinkafa ba, wasu badu yarda da mu ba. Gashi a Auyo ,jihar Jigawa, kuna iya ganin gonakin shinkafan da za’a a iya girban ton 1.2million na shinkafa.
“Wannan karamar Hukuma daya kacal kenan cikin 27 a jihar Jigawa, kowani dan Najeriya zai samu shinkafa mai kyau, ba wanda aka ajiye na shekara 7 a kasar waje ba.
“Babu wata hanyar raya mutanen karkara da yafi haka. Bamu bukatan cigaba da shigo da shinkafa malalaci daga wasu kasashe. Gwamnonin na kokarinsu wajen ganin cewa anyi noman shinkafa sosai a jihohinsu. Ba da dadewa ba zamu zama manyan masu fitar da shinkafa.Alabama.”
Source. Naij Hausa
Title :
Najeriya Zata Fara Fitar Da Shinkafa Kasar Waje - Ogbeh
Description : Ministan aikin noma, Cif Audu Ogbeh ya bayyana cewa Najeriya takusa ta fara fitar da shinkafa mai kyau zuwa kasar waje da sairan sassan duni...
Rating :
5