A yammacin jiya ranar Talata ne 22 da ga watan Nuwamba bangarorin biyu suka sanya hannu kan kwangilar a Abuja.
Babban sakatare a ma’aikatar ayyuka da gidaje da wutar lantarki Injiniya Magaji Abdullahi Gusau ne ya rattaba hannu a madadin gwamnatin tarayyar.
Yayin da mai bai wa shugaban kamfanin na Dangote shawara Injiniya Joseph Makoju ya sa hannu a madadin kamfanin, yana mai cewa “babban cigaba ne a tarihin Najeriya”.
Kamfanin ya ce watanni 24 ne lokacin da aka amince kare kwangilar, amma ya ce ya kudiri aniyar kammala wa a cikin watanni 16.
A wani labarin kuma, alkalumman da hukumar Kiddidiga a Najeriya ta fitar na cewa tattalin arzikin kasar ya sake samun koma baya a cikin watanni uku da suka gabata sakamakon hare-hare da ake kai wa kan bututun mai a yankin Neja Delta da kuma karanci kudaden waje a hannun ‘yan kasuwa.
Hukumar ta ce tattalin arzikin ya kara samun koma baya ne da sama da kashi 2.
Najeriya dai ta fada cikin matsalar tattalin arziki ne sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya inda farashin ya yi mugunyar faduwa daga dala 100 zuwa kasa da 50.
Hare haren da kuma tsagerun Neja Delta ke kai wa ya kara dada haifar da matsalar tattalin arzikin kasar da ke dogaro da arzikin mai.
Gwamnatin shugaba Buhari dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya
Title :
Najeriya Ta Daukewa Dangote Biyan Haraji
Description : A yammacin jiya ranar Talata ne 22 da ga watan Nuwamba bangarorin biyu suka sanya hannu kan kwangilar a Abuja. Babban sakatare a ma’aikatar...
Rating :
5