Kuma Za Mu Ci Gaba Da Yi Masa Biyayya, Cewar Sarkin Kano
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda shine Sarkin Yakin Sarkin Musulmi kuma shugaban kwamitin taron bikin cikar Sarkin Musulmi shekaru goma a karagar mulki, ya mika godiyarsa ga Allah na kasancewar Mai Alfarma Sa'ad Abubakar a matsayin Sarkin Musulmi.
Mai Martaba Sanusi, wanda ya bayyana hakan a wurin bikin cikar Sarkin Musulmin shekaru goma akan mulki, ya kuma kara da cewa za su ci gaba da yin biyayya ga Sarkin Musulmin kasancewar sun yaba da salon mulkinsa don haka a koda yaushe ya umarce su da yin ayyuka za su bi umarninsa.
Sarki Muhammadu Sanusi II, ya kuma kara da cewa, sune suka ga ya dace su hada wannan gagarumin taron, duk da cewa Sarkin Musulmin bai bukaci hakan ba.
Rariya
Title :
Mun Yaba Da Shugabancin Sarkin Musulmi - Sarkin Kano
Description : Kuma Za Mu Ci Gaba Da Yi Masa Biyayya, Cewar Sarkin Kano Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, wanda shine Sarkin Yakin Sarkin Mus...
Rating :
5