Daga Jaridar Rariya
Rikici a wannan masallaci na Sultan Bello da ke Kaduna ba sabon abu bane saidai rikicin na baya-bayan nan ya sami Asali ne ranar babbar Sallar da ta gabata da safe a lokacin da aka hadu domin gudanar da Sallar Idi tsakanin magoya bayan Dakta Ahmad Gumi da kuma na Limamin masallacin, Shaikh Balele Wali.
Hargitsin ya auku ne sakamakon fisge abin magana da Shaikh Balele Wali ya yi daga hannun Dakta Ahmad Gumi a lokacin yake gudanar huduba, inda shi kuma ya sa aka fitar masa da Limamin daga cikin masallacin, lamarin da ya haifar da rikicin a cikin masallacin.
.
Tun da farko an tsara za a yi Sallar Idi ne a filin da aka saba gudanarwa da misalin karfe 8:45, amma kuma sai hadari ya taso, don haka sai aka koma cikin masallacin domin gudanar da Sallar, kamar yadda tsohon Gwamnan jihar Kano, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya ba da shawara.
.
Da misalin karfe 9:00 aka fara sheka ruwa, abin da ya sa Liman bai iso ba. Ganin an kara mintuna 15 a kan yadda aka saba gudanar da Sallah, sai wasu mutane da ke wajen, irin su Sanata Ahmad Aruwa, Alhaji Dakta Lema Jibril, Alhaji Ali Sarkin Motan Sardauna da dai sauransu, suka ba da shawarar a wakilta Dakta Ahmad Gumi ya ba da Sallah.
.
Kafin nan dai an bukaci Na’ibi ya jagoranci Sallar, amma sai ya ki yarda, saboda yana gudun kar hakan ya haifar da matsala tsakanin sa da babban Liman, Shaikh Balele Wali.
.
Shi ma kansa kafin Dakta Ahmad Gumi ya amince da bukatar, sai da ya nemi ra’ayin jama’ar da ke cikin masallacin, inda suke ce sun amince ya jagoranci Sallar don a sallami jama’a su koma gida.
.
Ana cikin Sallar raka’a daya, sai Shaikh Balele Wali ya shigo, sai ya tsallo jama’a ya iso sahun gaba, inda ya kabbarta tasa Sallar. Bayan an idar kuma, sai Shaikh Ahmad Gumi, wanda ya jagoraci Sallar ya fara huduba kamar yadda aka saba. Amma Shaikh Balele Wali na idar Sallar sai ya fizge abin maganar daga hannunsa, ya ce;“Ba za ka yi hudubar ba”.
.
Nan take hayaniya ta kaure a masallacin, ’yan agaji da wasu magoya bayan Dakta Ahmad Gumi suka yi sama-sama da Shaikh Balele Wali suka yi waje da shi suka kai shi wani daki suka kulle.
.
Har takai ga Liman Balele ya samubuguwa a goshin sa saboda wutsulwutsul da ya rika yi, wanda hakan ya kara fusata magoya bayan Shaikh Balele Wali, inda hayaniyar ta kara ta’azzara. Jama’a dai sun tafi gidajensu ba tare da an gudanar da hudubar ba.
.
Wannan dai wata alama ce da ke kara fito da irin zaman doya da manjan da aka jima ana yi tsakanin magoya bayan bangarorin biyu, wanda ya samo asali tun bayan da Saudiyya ta sako Dakta Ahmad Gumi daga gidan kaso sakamakon daurin da ta yi masa.
.
Samun hargitsi a wannan masallacin a kan Limanci ba bakon abu ba ne, irin haka ta sha faruwa da Shaikh Ahmad Sunusi Gumbi, wanda wani lokacin sai ya yi sujuda ma ake dauke shi a yi waje da shi, abin da ya tilasta masa gina nasa masallacin a kofar gidansa.
Title :
Me Ya Jawo Hargitsi A Masallacin Sultan Bello Kaduna?
Description : Daga Jaridar Rariya Rikici a wannan masallaci na Sultan Bello da ke Kaduna ba sabon abu bane saidai rikicin na baya-bayan nan ya sami Asal...
Rating :
5