Watarana acikin garin Baghdad akwai wani babban kafiri wanda bai yarda da tauheedi ba, kuma bai yarda da cewa akwai Allah ba.
Har ma ya kirkiri wasu tambayoyinsa na shirme yana ta neman wanda zai amsa masa su. Duk Maluman garin sun kyaleshi basu daukeshi da muhimmanci ba, shi kuma yana ci gaba da bankaurarsa.
Alokacin nan Imam Abu Hanifah (rah) yana yaro Qarami bai fi shekara goma ba. Watarana yazo wucewa sai yaji mutumin nan yana da kurarin cewa wai Musulmai sun kasa amsa tambayoyinsa.
Sai Imam Abu Hanifah ya matsa kusa dashi yace masa "In sha Allahu ni zan amsa tambayoyin naka komai wahalarsu".
Mutumin ya amsa gayyatar, Kuma Jama'a suka cika da mamaki. Ta yaya wannan 'dan Qaramin yaro zai iya jayayya da Kafirin nan wanda manyan Maluma suka kasa ja dashi!
Da ranar Mukabalar tazo sai Jama'ar garin gaba daya suka taru a wani fili a tsakiyar garin Baghdad wanda dama anan ake gabatar da duk wani Muhimmin taro.
Sai shi wannan kafirin ya hau kan tudun dake tsakiyar taro. Sannan ya bude muryarsa ya jefo tambayarsa ta farko zuwa ga Abu Hanifah kamar haka :
"SHIN MENENE ALLAHN NAKU YAKE YI A DAIDAI YANZU?"
Abu Hanifah ya tsaya yayi tunani na 'yan mintuna kadan, sai yace ma mutumin "To ina so kai ka sauko Qasa, ni kuma in hau sama sannan in baka amsarka".
Wannan yaro Qaramin yaro 'dan shekara goma (wato Imam Abu Hanifah) ya hau saman kan tudun sannan yace "Ya Allah kaine shaida gareni agaban duk wadannan Mutanen cewar na shaida lallai yanzun nan kai ka Qaddara saukowar wannan kafiri zuwa Qasa, kuma ka Qaddara cewar Mumini zai hau sama (wato zai daukaka akansa)".
Da Mutane ('yan kallo) suka ji wannan amsar ta fito cikin fasaha daga bakin Abu Hanifah, sai suka fara kabbara "Allahu Akbar!" Allahu Akbar!"
Tun daga nan kafirin nan ya fara ganin Qaskanci. Amma sai ya sake jefowa tambayarsa ta biyu "SHIN MENENE YAKE RAYE KAFIN ALLAHN NAKU?" (Subhanallah).
Imam Abu Hanifah (rah) yayi tunani zuwa wani lokaci sai yace ma kafirin ya Qidaya masa lambobi daga goma zuwa Qasa.
Sai kafirin ya fara "Goma, tara, takwas, bakwai, shida, biyar, hudu, uku, biyu, daya, sufiri"
Sai yaron (wato Imam) yace masa "Shin me ka gani bayan sufiri (wato zero)?". Mutumin yace "Babu komai kafinsa, ni ban sani ba".
Da jin haka sai Imam yayi murmushi yace masa "To gashi nan ka riga ka bama kanka amsa.. Hakika Allah shine rayayye kuma dawwamamme. Babu kowa kuma babu komai kafinsa".
Daga wannan sai waje ya rude da kabbara, suna Qara jinjina ma Imam Abu Hanifah (rah).
Kafirin nan zuciyarsa ta harzuka, ransa ya baci. Sai ya jefo tambayarsa ta Qarshe "SHIN YANZU WAJEN INA (WACCE KUSURWA) ALLAHN NAKU YAKE KALLO?" (Shin gabas yake kallo ko yamma ko kudu ko Arewa?).
Imam Abu Hanifah bayan yayi tunani zuwa wani lokaci sai yace a kawo masa Fitila (Aci-balbal ko kuma kyandir). Da aka kawo masa sai ya damka wa kafirin nan. Yace masa ya kunna masa.
Bayan kafirin ya kunna kyandir din sai ya tambayi Imam to menene dalikin haka?.
Sai Imam Abu Hanifah yace masa "Shin wanne waje ne wutar hasken kyandir din nan take kallo?"
Sai kafirin yace "Tana kallon dukkan kuskuwoyi ne. (wato gabas, yamma, kudu, arewa, sama da Qasa) Babu inda bata kallo"
Sai Imamu yace masa "Ai ka riga ka amsa tambayarka. Hakika Hasken Allah ya mamaye ko ina. Yana nan ako ina, babu wajen da babu shi".
Daga nan sai mutane suka rude da kabbarori "Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!".
Shi kansa wannan kafirin yayi mamakin ilimi da basirar yaron nan. Don haka anan wajen ya furta kalmar Shahada, ya zama Musulmi kuma ya zama Almajirin Imam Abu Hanifah (ra).
Yardar Allah ta tabbata gareka Ya Imam Abu Hanifah. Allah ya saka muku da alkhairi bisa hidimar da kukayi ma addininsa.
Ya Jama'a wadannan fa sune wadanda suka yiwa addinin Allah hidima, suka rairayo mana garin Ilimi, suka dafa mana tuwonsa yanzu muke ci.
Amma abun Mamaki sai kaji mutum ya hura lasifika yana kushesu yana fadin cewa basu iya ba, shi ya fisu iyawa, ko kuma Malaminsa ya fisu.
Su fa sun rayu ne acikin mafiya alkhairin zamanunnuka, a Qalla dai sun riski wadanda suka ga Sahabbai. Kuma duk Mutanen da sukayi zamani dasu sun tabbatar da nagartarsu da gaskiyarsu.
Allah shi bamu albarkar masu albarka. Ameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP -1 Juma'ah 11-11-2016 (11-02-1438).