Kashewa, sacewa, tare da barnata dukiya mai dinbin yawa na cigaba da mamaye yankuna da sassa na jihar Zamfara. Kauyukan j8har Zamfara sun zama tamkar wani sansanin yaki, sun kasance wani wuri da rayuwa take da matukar wahalar gudanarwa.
Malam idan ka zagaya a mafi yawan kauyukan jihar Zamfara hankalinka zai yi matukar tashi, zuciyarka za ta buga sosai tamkar za ta fito waje, tsigar jikinka za ta tashi sakamakon yadda rayawu ta sukurkuce, halin kunci da rashin tabbas ya dabaibaye al'umma kai har ma da dabbobinsu.
Kauyukan juhar Zamfara sun zama kufai mutane sun gudu sun bar gidajensu, an sace dukiyoyinsu, an kona gidajensu babban abun bakiciki yanzu kuma mutane ne da kansu ake sacewa lunguna da sakuna.
Mafi yawan manoma, masu gonakki a kauwukan jihar Zamfara sun yi noma sosai amma sun lamunci su kauracewa duk abunda suka noma ya lalace a gona domin gudun kada su je gonar a saces u.
Mummunar dabi'ar garkuwa da mutane tare da neman kudaden fansa ta yi kamari sosai inda ake tare 'yan kasuwa a saman hanya a sace su, ana iske manoma a gona a sace su kai har wadanda ke kwance a gidajensu ana isko su har can a sace su, tare da neman makudan kudade kafin a sake su kasancewar yanzu ita kadai ce hanyar data rage ga barayin shanu wajen samun kudi domin yanzu duk shanun sun kare.
Kusan yanzu babu wata rana da ba za a samu rahoton kisa ko sace al'ummomi daban daban ba a jihar Zamfara musamman a garuwaruwan Magami, Yarkwana, Bindin, Dansadau, Dangulibi, Galadi, Yartasha, Anka, shinkafi, Maradun, Maru, Dankurmi, B/Magaji kai har ma da Gusau babban birnin jihar, wanda a cikin wata biyu ana zargin an kashe tare da sace mutane sama da 200.
Wallahi al'amarin tabarbarewar tsaro ya yi kamari a jihar Zamfara ya wuce duk yadda ake tsammani, abune wanda ya fi karfin a saka siyasa a ciki, abu ne wanda ya shafi kowa da kowa, abune wanda ya kamata mu tashi tsaye wajen, kira, addu'o'i, gyara halaye da dai sauransu wajen tabbatar da kawo karshen wannan lamari.
A bangaren gwamnati ba za mu ce ba sa kokari ba, amma maganar gaskiya akwai sakaci domin za ka ji a kafafen yada labarai ana cewa ana daukar mataki amma a zahiri abun ba haka bane. Ya zama wajibi ga gwamnati da musamman gwamnan jihar Zamfara A.A Yari ya dawo ya tare a jihar Zamfara ya mayar da hankalisa sosai akan wannan matsala kasancewar sa shine jagora.
Yakamata Gwamna Yari ya yi amfani da kusancin da yake da shi da shugaban kasa Buhari wajen bayyana masa gaskiyar lamari akan bukatar agajin gaggawa akan lamarin tsaro a jihar Zamfara, haka su ma 'yan majalisun mu na tarayya su sani cewa su ma akwai nauyi akan kawunasu game da wannan lamarin.
Allah ya kawo mana wanzuwar zaman lafiya a jihar Zamfara da kasa baki daya.
Na tabbata su dai jami'an tsaro kayan aiki da kuma umarni kawai suke jira.
Daukar matakin gaggawa akan wannan lamarin ya zama wajibi domin gudun inda abun zai kai nan gaba matukar aka zura ido.
Title :
Jihar Zamfara Na Bukatar Agajin Gaggawa Akan Matsalar Tsaro
Description : Kashewa, sacewa, tare da barnata dukiya mai dinbin yawa na cigaba da mamaye yankuna da sassa na jihar Zamfara. Kauyukan j8har Zamfara sun z...
Rating :
5