Bayan kwanaki da sace tsohon ministan harkokin kasashen wajen Nijeriya, Ambasada Bagudu Hirse, wanda wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace shi a Kaduna, a lokacin da ya je yi wa Mamman Daura ta'aziyyar rasuwar tsohon Sarkin Musulmi Sultan Ibrahim Dasuki.
Minista Samuel Pukat, wanda yana tare da Ambasada Bagudu Hirse a lokacin da aka sace shi, ya shaidawa kafar watsa labarai ta Premium Times cewa, wadannan 'yan Bindiga da suka sace tsohon minista Hirse sun sake komawa gidan Mamman Daura.
A rahoton kamfanin dillancin labarai na kasa NAN na ranar Litinin, sun tabbatar da cewa, wadanda da suka sace tsohon ministan sun yi waya da iyalansa, inda Minista Samuel Purkat ya bayyana cewa, sun fara kira na ne, kuma muryar Bagudu Hirse ne na fara ji a layin, kafin wadanda suka sace sa suka dauki wayar", ace warsa. Amma dai Minista Samuel ya ki bayyana abin da suka tattauna da mutanen.
Source Zuma Times Hausa
Title :
Iyalan Tshon Ministan Da Aka Sace Sun Yi Waya Da Wadanda Suka Sace Ministan
Description : Bayan kwanaki da sace tsohon ministan harkokin kasashen wajen Nijeriya, Ambasada Bagudu Hirse, wanda wasu 'yan bindiga da ba a san ko su...
Rating :
5