Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar Democrats daga kowacce kabila su fito su zabi Hillary Clinton, yana mai gargadin cewa ‘yan Republic da ma sauran al’umar duniya za su shiga uku idan Donald Trump yayi Nasarar Lashe zaben shugaban kasa da za’a kada a watan nan.
Obama ya shaida cewa Trump hatsari ne ga ‘yancin kasar na walwala.
Shugaban na Amurka yayi wannan bayanin ne a wajen yakin neman zaben Hillary Clinton a jihar North Carolina.
Sai dai Mista Trump ya ce ya kamata Mista Obama ya daina yi wa Clinton yakin neman zabe, ya mayar da hankali kan mulkin kasarsa.
Title :
Har Idan Trump Ya Lashe Zabe Lallai Duniya Zata Shiga Uku – Obama
Description : Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar Democrats daga kowacce kabila su fito su zabi Hillary Clinton, yana mai gargadin c...
Rating :
5