A yayinda kamfanin zauren zumunta na facebook karkashin shugaban kamfanin Mark Zuckerberg ke kokarin kawo karshen masu sojan gona "Scammers" da shafukan bogi masu yada labaran kanzon kurege da kage sai kuma ga bullar sabuwar zamba da masu kusten suka bullo dashi.
A cikin sabbin dabarun da wadannan mutane na bogi masu zamba cikin aminci "scammers" ke amfani dashi sun hada:-
1. Suna kirkirar shafukan bogi da sunayen fitattun gidajen jarida misali BBC, Hausa Times, Rariya da dai sauransu. A binciken da mukayi mun samu a yanzu haka akwai shafukan Rariya na bogi fiye da 200 a facebook. Sai ayi hattara!
2. Suna kirkirar akawun na facebook ko shafuka da sunan fitattun mutane kamar shugaban kasa, ko Gwamna ko sunan wani fitaccen dan siyasa ko hamshakin mai kudi ko attajirin dan kasuwa ko jarumin finafinai ko wasanni ko Malamin addini. Shima suna amfani da wannan wajen zambatar mutane ko kuma bata sunan mai wannan suna. Don haka a rika kiyayewa ko lura sosai game da mu'amala da wadannan shafuka.
3. Suna kwace facebook akawun din mutum su gogeshi daga facebook gaba daya ko kuma suyi masa kutse. Suna da hanyoyi da dama da sukeyin haka abunda yafi shine mutum yayi amfani da lambar sirri "password" mai karfi ta hanyar amfani da haruffan @$-+*"#?!=,$4 da dai sauransu. Sannan mutum ya boye bayanin cikakken ranar haihuwarsa wato "Date of birth" a karshe kuma ana shawartar mutum ya sanya sunansa na haihuwa yadda yake a jikin fasfo dinsa ko takardun makaranta.
4. Kada ka kuskura ka bawa wani lambar sirrin akawun dinka, sannan kada ka sanya wanda baka sani ba cikin admin din shafinka. Shima suna amfani da wannan damar wajen yi maka barna a shafinka ko akawun dinka. Misali ina amfani da Mashkur24 kuma shafina ya kai fiye da mutane dubu 89 bayan da masu kutse sukayi sa'ar samun lambar sirrin daya daga cikin admin din shafin shikenan suka koremu "suka ciremu daga admin" suka mallake shafin suna zambatar mutane da yada badala wanda hakan bata suna ne kuma akwai hadari sosai.
5. Ka kiyayi shiga rariyar likau "Link" kasafai ko kuma yawan musayar sako "chat" da bakon da baka taba ganinsa ba ko kuma bai taba sanya hotonsa a akawun dinsa na facebook ba hakanan ka guji bayar da lambar wayarka ko sanya lambarka kasafai a shafukan sada zumunta. Akwai hadari sosai.
6. Ka guji yawan bayyana inda kake ko ambatar adreshin ka ko inda zaka. Wannan ma akwai hadari sosai.
7. Akwai shafuka amintattu da zaka samu labarai game da dukkan abunda ya faru cikin sauki kuma a harshen hausa misali Rariya, da sabuwar jaridar Hausa Times waccen idan kayi "Searching" din sunan zaka ganta kayi LIKE domin samun labarai na gaskiya masu inganci ba sai ka kai kanka shafukan bogi ba.
Daga Hausa Times
Title :
Hanyoyi 7 Da Zaka Kare Kanka Da Facebook Dinka Daga Yan 419
Description : A yayinda kamfanin zauren zumunta na facebook karkashin shugaban kamfanin Mark Zuckerberg ke kokarin kawo karshen masu sojan gona "Sca...
Rating :
5