Daga Habu Dan Sarki
Gwamnan jihar Abdulaziz Yari ya ba da umarnin katange dukkan tashoshin mota dake jihar, musamman a babban birnin jihar Gusau, tare da kafa ka'idojin binciken jama'a da kayansu, yayin shiga da fita jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne, a wani taro na musamman da ya yi da shugabannin kungiyar direbobin motar haya ta NURTW tare da kwamishinan 'yan sanda na jihar da wakilan hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta kasa, FRSC.
Gwamna Yari ya kara jaddada aniyar gwamnatin sa ta nuna halin ba sani ba sabo wajen yaki da tabarbarewar tsaro a jihar.
Title :
Gwamnatin Zamfara Kafa Dokar Hana Amfani Da Budaddiyar Tasha
Description : Daga Habu Dan Sarki Gwamnan jihar Abdulaziz Yari ya ba da umarnin katange dukkan tashoshin mota dake jihar, musamman a babban birnin jihar...
Rating :
5