Wani mutum mai suna Saminu Bara'u dan kimanin shekaru talatin dake zaune a garin Maraban Jos a Kaduna mai sana'ar tukin mota, ya gamu da a jalinsa a ranar Larabar da ta gabata bayan wani dan sanda ya dirka masa alburushi a kirjinsa.
Mamacin ya rasu ya bar 'ya'ya uku ne da mace daya.
Rahotanni sun nuna cewa wannan mamaci kafin wannan rana daman ya samu hatsari inda kusan watanni uku ba ya fita ko ina sakamakon karayar da ya samu a hatsarin.
Amma da yake kwana ya kare kawai a wannan rana ya ce a kai shi waje domin ya sha iska kuma ya ga gari ashe dai iskar karshe zai sha. Inda a daidai wannan lokaci su kuma jami'an 'yan sanda sun fito sintiri, jama'a na ganin su sai suka ranta a na kare kowa ya gudu, shi kuma mamacin saboda karayar dake kafarsa ya sa ba zai iya gudu ba. Inda da zuwan wadannan 'yan sanda kawai sai daya daga cikin 'yan sanda wanda ake yi wa lakabi da Ofisa Kura ya dirka masa harsashi a kirji.
Saidai majiyar ta mu ta kara da cewa an kama wannan dan sanda kuma ana kan binkice.
Title :
Graphic Photos: Dan Sanda Ya Bindike Wani Majinyaci Har Lahira A Kaduna
Description : Wani mutum mai suna Saminu Bara'u dan kimanin shekaru talatin dake zaune a garin Maraban Jos a Kaduna mai sana'ar tukin mota, ya ga...
Rating :
5