A daidai wannan zamani da al’amura ke canzawa ta hanyar sadarwa cikin gaggawa, Hukumar Kula da Tattara Bayanan Filaye ta Kano (KANGIS), da Kungiyar Tarayyar Turai (EU), da Hukumar Raya Kasashen Duniya ta Birtaniya (DFID), sun cimma yarjejeniya domin ba da tallafi na saukaka wa masu gida mallakar takardun shaidar gidajensu da aka kiyasta sun kai kimanin miliyan biyu da rabi.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Sabeyo Malandi Umar Kura, mukaddashin darakta na hukumar KANGIS lokacin da yake hira da manema labarai a ofishin sa da ke Kano amakon da ya gabata.
Ya ce hukumar tana karkashin ma’aikatar kasa da safiyo ne, kuma an kirkire ta ce domin ta dace da kalubalen zamani na saukakawa jama’a mallakar takardar shaidar gida a ko ina mutum yake a Jihar Kano, sabanin a baya da abin yake daukar tsawon lokaci kafin a samu takardar.
Haka kuma ya kara da cewa babban aikin wannan hukuma ta su shi ne sanin dukkan wani abu da yake doron kasa da ke Jihar Kano wadanda suka hada da gidaje, kasuwanni, kamfanoni, hanyoyin zirga-zirga, asibitoci, kotuna, makarantu da dai sauransu.
Leadership Hausa
Title :
Gidaje Miliyan Biyu Za Su Samu Takardun Mallaka A Kano
Description : A daidai wannan zamani da al’amura ke canzawa ta hanyar sadarwa cikin gaggawa, Hukumar Kula da Tattara Bayanan Filaye ta Kano (KANGIS), da ...
Rating :
5