Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya musanta zargin cewa yana da hannu cikin rashawa a kasar nan inda yace kalubalantar shi da ake yi yana da alaka da rigimar da ke tsakanin shi da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake hira da jami'an yada labarai na hukumar ta EFCC wanda suka buga labarin a mujallar su na yakar rashawa.
Da yake amsa tambaya dangane da kalubalantar shi da rashawa yayin da ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2006, Atiku ya ce idan da yana da laifi da hukumomin yaki da rashawa sun tabbatar da laifin shi bai cin bincike da suka yi akan hakan.
"Ina tuna madogarar zargin da aka dogara da shi shine farar takadda da aka kulla a karkashin mulkin mu wanda na taimaki EFCC bincike da wasu ministoci da na kalubalanta a kotu a wancan lokacin.
"Kotu ta kori karar a matsayin bita da kullin siyasa kuma har yanzu babu wanda ya taba kama ni da rashawa," Inji tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Da yake amsa tambayoyi akan zargin rashawa da aka jingina a cikin littafin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufa'i, Atiku ya ce Elrufa'i bai kawo hujja ko kwara daya ba da yake nuna shi yana da hannu a cikin rashawa.
"Su din ne kuma (su Elrufa'i) suka ba ni kyautukar hannun jari a lokacin da nake mataimakin shugaban kasa amma naki amsan su. Na rubuta musu wasika cewa bai dace ba na karbi kyautukan, to anan daga ina ne rashawan ya bullo?" inji Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya kuma yi bayani akan badakalar kudi naira miliyan hamsin (N50m) wanda ya hada da Sanata mantu, Jonathan Zwingina da wasu yayin da ake tantance Malma Nasiru Elrufa'i a matsayin ministan tarayya. Atiku yace bayan da Elrufa'i ya same shi da kukan sanatoci sun ki bada lamuni akan zaben shi a matsayin minista, sai ya kira Mantu da wasu ya sanya baki a lamarin.
"Sannan shugaban kasa a lokacin ya binciki wannan magana inda ya samu cewa dukkan sanatoci ne suka samu tallafi daga asusun yakin neman zabe wanda nake shugabanta, to a ina rashawa yake a nan?" Inji Atiku Abubakar.
Title :
El-rufai Ya Ba Ni Kyautar Hannun Jari Amma Naki Karba, - Atiku
Description : Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya musanta zargin cewa yana da hannu cikin rashawa a kasar nan inda yace kalubalantar...
Rating :
5