Dan takarar Shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya lashe zaben kasar da aka yi ranar Talata.
Mista Trump ya lashe zaben ne bayan da ya samu nasarar cinye kujerun wakilai sama da 270 a jihohi 50, a inda ya kayar da abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton.
Trump, wanda ya gabatar da jawabin amincewa da yin nasara, ya ce Clinton ta kira wo shi a wayar tarho inda ta taya shi muranr lashe zaben.
A cewarsa, zai mayar da hankali wajen ganin ya sake gina Amurka, yana mai cewa muradin kasar su zai sanya farko a kan komai.Ya kara da cewa zai yi aiki tukuru wurin hada kan jama'ar kasar, sannan ya nemi hadin kan wadanda suka yi adawa da shi.
Ya kuma sha alwashin ganin ya saka Amurka a gaba a duk huldar da zai yi da kasashen waje.
Sai dai ya ce zai yi alaka mai kyau ta mutuntaka da sauran kasashe.
Nasararsa ta zo da matukar mamaki saboda dukkan kuri'un jin ra'ayin jama'a sun nuna Clinton na bayansa.
Title :
Donald Trump Ya Zama Sabon Shugaban Kasar Amurka
Description : Dan takarar Shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya lashe zaben kasar da aka yi ranar Talata. Mista Trump ya lashe...
Rating :
5