Sabon zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya goge kalaman batancin da yi akan Musulmi da Musulunci daga shafinsa na facebook bayan da ya yi nasarar cin zabe.
Tun dai karshen shekarar 2015 Trump ke ta kira ga shugaba Obama da ya gaggauta hana Musulmi shiga kasar Amurka, wanda a cewar shi Trump din Musulmi ne suka haifar da 'yan ta'adda a duniya.
A ranar 10 ga wannan watan na Nuwamba ne dai masu kula da shafin na Trump suka goge kalaman bayan da aka sanar a hukumance cewa Trump ne ya yi nasara a zaben.
Donald Trump dai ya bayyana cewa idan ya har ya yi nasara to, zai dauki matakin hana Musulmi shiga Amurka tare da sa ido ga Musulmi 'yan asilin kasar.
Yanzu dai babu wani rubutu a shifin na Trump da ke nuna kyamar Musulunci ko cin fuska ga Musulmai.
Rariya
Title :
Donald Trump Ya Share Furucin Da Ya yi Akan Musulunci Daga Shafin Sa Na Facebook
Description : Sabon zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya goge kalaman batancin da yi akan Musulmi da Musulunci daga shafinsa na facebook bayan d...
Rating :
5