Wasu daga cikin ‘Yan Kungiyar Bakassi Strike Force sun nemi afuwa wajen Hukumar DSS masu farar hula na Kasar. Tsagerun Neja-Delta suna neman ayi masu rai bayan da suka ji haza wajen fada da Rundunar Sojin Kasar.
Tsagerun Neja-Delta na Kungiyar Bakassi Strike Force sun kuma ajiye makaman su da nufin ajiye yaki inji Jaridar Punch. Tsagerun Neja-Delta na neman sulhu ne, a ba su lamuni. Rundunar Sojin Kasar ta kai hari ga Tsagerun da ke boye a Yankin Akwa-Ibom da Delta, hakan ta sa aka kama da daman a Tsagerun.
Tsagerun Neja-Delta da dama dai sun rasa rayukan su wajen fada da Sojojin Kasar, hakan ta sa wasu suka mika kan su, suna neman afuwa. Shugaban Rundunar Operation Delta Safe-masu kokarin ganin an kauda fitina a Yankin na Neja-Delta, Laftana-Kanal Olaolu Marcelinious Daudu yace Tsagerun sun ajiye makamai, sun shirya zaman sulhu.
Benjamin Ene, wanda shine Shugaban Kungiyar Bakassi Strike Force yace a shirye suke da yin sulhu da Hukuma. Laftana-Kanal Olaolu Marcelinious Daudu yace dai an kashe Tsageru, yayin da kuma wasu 2 suka samu rauni, wasu 7 kuma suna hannu yanzu haka a Garin Kumfari da ke kusa da Garin Idama na Jihar Rivers.
Title :
Don Allah Ku Mana Rai, Tsagerun Neja-Delta Sun Roki DSS
Description : Wasu daga cikin ‘Yan Kungiyar Bakassi Strike Force sun nemi afuwa wajen Hukumar DSS masu farar hula na Kasar. Tsagerun Neja-Delta suna neman...
Rating :
5