Kungiyar direbobin Tirelolin masu dakon shanu daga kasuwar shanu ta kasa da kasa na garin Mubi, dake jihar Adamawa sun yi barazanar shiga yajin aiki saboda abin da suka kira tsangwama da cin mutunci da gallazawa na jami’ian tsaro akan hanyoyi don karbar na goro.
Shugaban kungiyar direbobin Tirelolin dakon shanu ta kasa reshen kasuwar Alhaji Malam Bappa, yace akalla kowacce Tirela da ta tashi daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya, na kashe Naira Dubu 200 zuwa Dubu 300 wajen baiwa jami’an tsaro na goro ko kuma su fuskanci wulakanci.
Ya ce yanzu haka suna duba yadda za su fitowa lamarin ganin cewa duk kokari da suka yi su ganar da hukumomin da abin ya shafa irin halin da suke fuskanta, amma kawo yanzu babu wani kwakkwarar mataki da suka dauka, shi ya sa suka ga ba su da wani zabi illa ta shiga yajin aiki.
Shugaban dillalan shanu Alhaji Usman Dan Mai Nagge, ya shaidawa Muryar Amurka cewa suna ta biyan kudade ga jami’an soji da ‘yan sanda ba tare da an basu risiti ba, zargin da kakakin soja runduna ta 28 na Mubi dake jihar Adamawa, Manjo Dadare da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Taraba ASP David Misal suka musunta.
Idan za a iya tunawa a watan Yunin wannan shekara wani karen motar wata Tirela ya rasa ransa lokacin da gardama ta kaure tsakaninsa da wani jami’in tsaro kan rashin mika na goro.
Title :
Direbobin Manyan Motoci Za Su Shiga Yajin Aiki Saboda Yawan Karbar Na Goron Da Jami'an Tsaro Ke Yi A Hannunsu
Description : Kungiyar direbobin Tirelolin masu dakon shanu daga kasuwar shanu ta kasa da kasa na garin Mubi, dake jihar Adamawa sun yi barazanar shiga y...
Rating :
5