Watakila ka samu sako daga kamfanin wayar da ka ke aiki da shi na cewar kamfanin zai kara farashin data daga ranar 1 ga watan Disamba, 2016. Wannan sako da ka samu dai kamar cika umarnin Hukumar Lura Da Harkokin Sadarwa Ta Kasa NCC ta bayar ga kamfaninnikan wayoyi na MTN, Airtel, Glo da Etisalat.
Wata majiya daga NCC din na cewa, hukumar ta NCC ta bayar da wannan umarni ne sakamakon matsin lamba da ta samu daga kananan kamfaninnikan da ke sayar da data da kuma sababbin shiga harkar da ke cewa su ba za su iya sayar da data a farashin da NCC ta yi umarni da a sayar da data a kwanakin baya na kobo 90 a kowane MB. Bayan da NCC ta bayar da umarnin na farko na karya farashin data, tuni dai manyan kamfaninnika suak bi umarni kuma suka ci gaba da sabon farashin ba tare da tashin hankali ba.
Amma bayan watanni kadan da farawar sababbi da kananan kamfaninnika, sai suka fahimci ba za su kai labari ba in suka ci gaba a kan farashin da muke sayen data a yanzu, wanda hakan ya sanya suka fara kokawa ga hukumar NCC.
Kananan kamfaninka a nan na nufin duk kamfanin da ke harkar cinikin data da karfin kwastomansa bai wuce kaso 7.5 cikin 100 na adadin kasuwar data ba. Su kuma sababbin kamfaninnikan da ke cinikin data su ne kamfaninnikan da ba su kai shekaru 3 da fara harkar ba.
Wannan dalili ya sanya hukumar NCC ta umarci da a kamfaninnikan da ke wannan harka ta cinikin data manyansu da kankana, tsofinsu da sababbinsu da su kara farashin data ta yadda kanana da sababbinsu za su samu riba
Wannan sabon farashi na data zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Disamba, 2016 kamar yadda majiyarmu ta tabbatar mana kuma kamar yadda manyan kamfaninnika irinsu MTN, Airtel, Globacom da Etisalat suka sanar da kwastomominsu
Source Alummata
Title :
Dalilin Da Ya Sa NCC Ta Umarci Kamfaninnikan Wayoyi Da Su Kara Farashin Data
Description : Watakila ka samu sako daga kamfanin wayar da ka ke aiki da shi na cewar kamfanin zai kara farashin data daga ranar 1 ga watan Disamba, 2016....
Rating :
5