Daga Khadija Garba Sansui
DANGANE DA RIKICIN KWANKWASIYYA DA GANDUJIYYA
Bayan daruruwan gaisuwa a gare ka da fatan kana cikin Koshin lafiya, ya aka ji da ayyukan ofis?
Maigirma Kwamishina na zabi hanyar rubuta maka budaddiyar wasika ne domin tunatar da kai wasu muhimman abubuwa da m al'ummar jihar Kano suke ganin laifin rundunar ka akai. Dangane da rikicin tagwayen Kungiyoyin siyasar nan na Kano Kungiyar da ba sa ga maciji da juna, wato Kungiyar Kwankwasiyya ta magoya bayan tsohon Gwamnan Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma Kungiyar Gandujiyya ta magoya bayan gwamnan Kano mai ci Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Saboda ba ni da wata hanya da ta wuce wannan.
Ranka ya dade rikicin wadannan kungiyoyi na siyasa a jihar Kano wato Kwankwasiyya da Gandujiyya ba sabon labari bane a kunnuwan rundunar 'yan sanda ta jihar Kano domin sau da dama mukan jiyo sanarwar haramta wasu tarurruka na wancan Kungiyoyi daga rundunarku saboda kare lafiya da dokiyar al'ummar Kano.
Saidai abunda ya daurewa ire-ire na kai shine yadda wancan haramcin yake aiki akan Kungiya daya tal wato kungiyar Kwankwasiyya. Ba mu taba jin kun haramta taron Gandujiyya ba duk da cewar kuna sane da irin tashin hankali da taron wancan kungiya yake haifarwa a Kano.
Ranar 20 ga Watan Agusta da ya gabata kungiyar Kwankwasiyya ta shirya taron aurar da Zawarawa 100 amma kwatsam sai muka ji rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta hana wannan taro, saboda wai ya yi daidai da ranar da Gandujiyya za ta gudanar wani taron tallafawa matasa 1000 da kayan sana'oi kuma duk da cewar yan Kwankwasiyya sune suka fara neman iznin gudanar da nasu taron kafin yan Gandujiyya su nema daga rundunar ku kuma kuka lamuncewa Kwankwasiyya ta je ta yi taronta, amma daga baya kuka ce kada Kwankwasiyya ta yi taron saboda dalilin da na fada a sama,
Hakan ya sa 'yan Kwankwasiyyar suka ce to ku ba su dama su gundar da nasu taron ranar 21 ga wata amma shi ma fafur rundunar 'yan Sanda ta ki yarda, karshe ma kuka ce gaba daya taron kun hana shi har illama sha Allahu. Haka nan 'yan Kwankwasiyya suka hakura aka daura auren a Msallatai daban-daban na cikin birnin Kano ba tare da da gudanar da taro ba.
Abunda ya kara bawa Kanawa mamaki shine yadda rundunarka ta Yan Sanda ta rufe gidan tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso wanda a ciki ne aka ajiye kayan dakin wadancan Zawarawa, bugu da kari har kwanan gobe ba mu ji inda Gandujiyya suka gudanar da wani taro na taimakawa matasa da kayan sana'oi ba. Dalili kenan da ya sa mutanen Kano suke fadin cewar dama hada baki aka yi da rundunarka ta Yan sanda domin hana wancan bikin Aure na Zawarawa.
Ranka ya dade Kwamishina ba wai iya wancan taron Kwankwasiyya na bikin Zawarawa kawai Rundunarka ta hana Kwankwasiyya ba, akwai tarurruka masu dumbin yawa da kuka hana kungiyar kwankwasiyya amma na dauki iya wancan ne domin na kafa Hujja dashi.
Yallabai na san kana sane da da wasu tarurruka a Kungiyar Gandujiyya take yi a ofishin jam'iyyar APC na Kano dake kan Titin Maiduguri kuma ka san yadda tarurrukan suka zamo barazanar zaman lafiyar mutanen wannan yanki, saboda babu wata rana da za'ayi wannan taro baka ga nau'i-nau'i na muggan makamai ba suna walankeluwa a wannan wuri kuma a gaban Jami'an rundunar 'yan sanda ta Jihar Kano ake daga wadannan makamai amma ba mu taba jin muryar rundunar tana Allah wadai da wancan taro ba ballantana har takai ga an dakatar dashi ko kuma rufe ofishin gaba daya ba, duk da cewar wata ranar ma riga a hannu takalmi a hannu mahalarta wannan taro suke barin wurin.
Wata ranar kuwa ma sai an yi wa wasu jina-jina saidai kaga motocin asibtin suna zaryar diban wadanda aka raunata, amma duk rundunarku ta yi shuru ta ki cewa uffan akai. To yau dai an yita ta kare domin a wajen wannan taro da aka gudanar yau Laraba 16/11/2016 an samu mummunar tashin hankali wanda rahotanni suke cewa ya yi sanadiyar rasa rai bayan jikkata al'umma da dama sakamon sakacin rundunar ku ta 'yan sanda.
Gaskiyar Lamari yanzu al'ummar jihar Kano da makota sun zuba idanu su ga wanne hukunci za ku dauka. Shin za ku dakatar da gudanar wancan tarurruka ne ko kuwa za ku ci gaba da zuba idanu ana wasan kura da zaman lafiyar al'ummar wannan yanki?
Allah dai masani ne akan komai kuma ya yi alkawarin yi wa kowa sakayya akan abunda ya shuka a wannan duniyar walau mai kyau ko akasin haka ranar da dukkan halittu za su taru a kotunsa.
Khadija Garba Sanusi Bauchi ita ce
Mataimakiyar Shugabar Mata ta kasa a Kungiyar Kwankwasiyya.
Title :
Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Kwamishinan Yan Sanda Na Jihar Kano
Description : Daga Khadija Garba Sansui DANGANE DA RIKICIN KWANKWASIYYA DA GANDUJIYYA Bayan daruruwan gaisuwa a gare ka da fatan kana cikin Koshin lafiy...
Rating :
5