Ban cika magana akan wani Mutum ko sana'arsa ko aikinsa ko halayyarsa ba, musamman lokacin da kowa ya ke qoqarin nuna kwarewarsa wajen iya sharhi, sharri, cusawa wasu haushi, nuna isa da watsa wa wasu laifi.
Amma dukkan kokarin da na yi na kaucewa maganar Jarumar Wasan Hausa, wato Rahama Sadau, sai da na sami kaina ina rubutu akai.
Dalilai biyu ne suka jawo min rashin hakurin na bar rubutu:
1- Kasancewar dole ne ko mun kin ko mun so akwai wanda wannan ci gaban nata (koda na mai hakan rijiya) zai burge shi, kuma yayi fatan ina ma shi/ita ma ace ta sami karbuwa da shahara kamar Jarumar.
Ina ma ace itama har wani cikin Malamai zai mata nasiha, ta yi watsi da kunnen uwar shegu da shi, ta kuma je ta samo Dalolinta ta kara suna, da fitowa da Hausawa filin 'yan rawa da waka da kida a fadin duniya.
Sannan uwa uba ni ma ina da 'ya'ya maza da mata wa'yanda ko yaya za su ji abinda ya faru da ita, su kuma nemi ra'ayina da fahimta ta kan mas'alar.
2- Kuma babban dalilin shine rubutun Malam Yakubu Musa wanda ya sa tattaunawa ta zo da batun mahaifiyarta ta nuna bata goyon bayanta cikin wannan shaharar, amma wai mahaifinta ne da 'yan uwansa suke daure mata gindi, saboda Nairori da Dalolin da suke samu ta wajen Jarumar 'yar tasu.
San nan K6asancewar Uwar bata tare da mahaifin, babu abinda za ta iya sai dai kawai ta zura mata na mujiya.
Sai dai Shahararriyar 'yar Jaridar nan, Hajiya Mairo Muhammad Mudi ta yi mamakin jin hakan, domin ita ta ga irin kamar goyon bayan da wannan uwar take bawa 'yarta a fili, da yanda take halartar wasu bukukuwa da 'yar, akwai mamakin ace wannan maganar ta fito ne daga bakin mahaifiyar.
San nan wasu ma sun dora laifin kacokan kan malamai, wai saboda sune suka tunzura ta, ta bi uwa duniya ta kara nausawa dajin Sambisar mawaqa da makada da masu rawar dandi.
Koma dai me za a ce ko a rubuta, kamar wanda suka shude kafin ta, za ta zama tarihi nan gaba ba da jimawa ba.
Mu kuma duk abinda muka fada, ko muka rubuta ko muka aikata, mu tarar da shi a littafinmu ranar kiyamah ba ragi ko kari.
Su kuma Iyaye da Allah ya ba su amanar 'ya'ya, sun yi bayani a gaban Allah da Mala'iku da Mutane da Aljanu a farfjiyar Kiyamah.
Allah ka6 kare mu da zuriyarmu daga zamiya, ka bamu ikon sauke amanar daka dota mana, ka sanyamu cikin bayinka nagartattu.
Source Zuma times
Title :
Ba Ni Na Kashe Zomon Ba - Rahma Sadau
Description : Ban cika magana akan wani Mutum ko sana'arsa ko aikinsa ko halayyarsa ba, musamman lokacin da kowa ya ke qoqarin nuna kwarewarsa waje...
Rating :
5