BANGAREN Shari'a na kasar Amurka ta karyata zargin da ake yi wa tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, cewa akwai zargin da ake yi masa a kasar ta Amurka, wanda ke jiran yanke hukunci.
A wani sakon Email da suka aiko wa jaridar Punch a ranar Juma'a, mai magana da yawun bangaren na Shari'a, Peter Carr, ya nuna jin dadinsu kan tuntubarsu da aka yi. Ya ce, bayan bincike kan abin da aka ce ana zargi, ya tabbatar da cewa, ba su da wani wanda suke zargi da wani laifi mai suna Atiku.
Wannan bayanin dai, yana da alaka da bukatar Jaridar Punch ta nema, domin ta sami tabbacin idan da gaske kasar Amurka na farautar Atikun kan zargin sama da fadi da dukiyar al'umma, da jibge su a can.
Dangane da zargin cewa wai kasar ta Amurka ta haramta wa Atikun shiga kasar kuma, kan zargin badakalar Halliburton, sun ce wannan wani batu ne daban, wanda ba za a bayyana shi ba.
Ya cigaba da cewa, al'amarin bayar da biza, wani sirri ne na musamman a dokokin kasar Amurka. "Amma idan kuna son karin bayani kan haka, ina ba ku shawara da ku tuntubi bangaren kwastam, da kula da kan iyakoki na wannan kasar, inji mai bada amsa.
Idan za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne, gwamnan jihar Kaduna Nasir El Rufa'i, ya zargi Atikun da kin zuwa kasar Amurka, saboda a cewarsa wai ana tuhumar sa da zargin safarar kudi.
Shi ma dai Atikun, ya zargi gwamnan na Kaduna, a cikin wata mujalla ta hukumar yaki da almundahana da ke fitowa a duk watanni uku, da laifin almindahana, a lokacin da ya ba shi gudanar da aikin shugabancin saida hannun jari na Transcorp.
Title :
Ba Ma Zargin Atiku Da Aikata Wani Laifi - Gwamnatin Amurka
Description : BANGAREN Shari'a na kasar Amurka ta karyata zargin da ake yi wa tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, cewa akwai...
Rating :
5