'Yan uwan marigayi Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali, wato kwamandan rundunar sojin kasar ta 272 mai kula da tankokin yaki, da 'yan Boko Haram suka kashe a jihar Borno sun zargi rundunar sojin kasar da rashin ba shi hutu.
Amina Abu Ali, kanwar Muhammad Abu Ali, ce ta yi wannan koke lokacin da wata kungiya mai rajin kare hakkokin sojin Nijeriya da suka rasa rayukansu a lokutan yaki ta je yi musu ta'aziyya a Kaduna.
A cewarta, "Muna fatan sojin Najeriya za ta kammala yaki da 'yan Boko Haram domin gudun ci gaba da asarar zaratan sojin kasar".
Ta kara da cewa ya kamata a canza lokacin da sojoji ke shafewa a fagen daga domin "idan sun dade a can akwai gajiya. Sojoji na nan ko'ina, ba wai wasu sojoji ne kawai za su yi wannan yakin ba".
Ta ce "Dan uwana ya zauna a Maiduguri tsawon shekara biyu, amma hutun mako biyu kawai aka ba shi."
A yayin da majiyarmu ta BBC ta tuntubi Kakakin rundunar sojin kasa kan wannan zargi, amma har yanzu ba ta samu amsa ba.
Muhammad Abu Ali ya rika samun karin girma akai-akai saboda jarumtarsa.
A ranar Litinin din da ta gabata ne aka yi jana'izar Muhammad Abu Ali tare da wasu sojoji hudu.
Sun mutu ne lokacin da suke kokarin dakile wani harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a barikin sojin kasar na 119 da ke garin Malam Fatori a jihar Borno.
Kafin rasuwarsa, Kanar Ali ya taka rawa sosai wurin kwato wasu garuruwa daga hannun Boko Haram, abin da ya sa aka yi masa karin girma.
Baya ga iyalan Kanar Ali, sojoji da dama da ke fafatawa a yankin Arewa maso Gabas, na kokawa kan rashin musanya su da karancin samun hutu.
Title :
Ba A Baiwa Kanal Abu Ali Isasshen Hutu Ba, Cewar 'Yan Uwansa
Description : 'Yan uwan marigayi Laftanal Kanal Muhammad Abu Ali, wato kwamandan rundunar sojin kasar ta 272 mai kula da tankokin yaki, da 'yan B...
Rating :
5