Musulmi a Kasar Isra’ila da kuma a yankunan Palastine da Isra’ilan take iko da su da kuma wasu sauran sassan duniya sun alakanta gobarar da ta mamaye kasar na tsawon kwanaki da fushin Ubangiji sakamakon yunkurin hana yin kiran sallah.
Kwamitin Ministocin Kasar Isra’ila ya kammala shirye-shirye don yin dokar da zata hana yin kiran sallah ta hanyar yin amfani da amsa kuwwa saboda abin da suka kira hana cikawa mutane kunne da rage takura musu. Wani bangare na dokar wacce tun a tsakiyar wannan watan na Nuwamba ake ta muhawara a kan ta kuma yana bukatar a rage murya sosai idan za a yi kiran Sallah a wasu sassan kasar.
Shafukan sada zumunta da na yanar gizo da dama na larabawa, musamman wadanda suke kewaye da kasar ta Isra’ila da jakadiya ta yi bincike a kansu, ya nuna cewar mutane da dama suna murna da barkewar gobarar inda wasu suke ta addu’ar kasar ta kone baki daya, abin da ya yi matukar bata wa gwamnatin ta Isra’ila rai. Ko a satinnan Jakadiya ta ci karo da
wani faifan bidiyo wanda bata gama tantance ingancinsa ba wanda ya nuna wani dan majalisar Isra’ila Muslmi yana kiran sallah a majalisar kasar duk da ihun da sauran ‘yan majalisa yahudawa suke ta yi masa kan ya daina.
Wutar dai tuni ta lafa inda hukumomi suka mayar da hankali waje ceto. Kusan mutane Miliyan 1.5 ko kuma 17.5% na yawan mutanen Isra’ila Musulmi ne, kodayake addinin da ya fi karfi a kasar shi ne Yahudanci.
Title :
An Alakanta Wutar Dajin da ta Mamaye Kasar Isra’ila Da Fushin Ubangiji
Description : Musulmi a Kasar Isra’ila da kuma a yankunan Palastine da Isra’ilan take iko da su da kuma wasu sauran sassan duniya sun alakanta gobarar da...
Rating :
5