Daga zuma times hausa
Wani rahoto da ke fitowa daga Gusau fadar gwamnatin jihar Zamfara ya na nuni da cewa, shiryen shirye sun kankama na kafa dokar hana yawon barace barace a fadin jihar.
Wannan dai wani mataki ne da gwamnatin jihar ke son dauka, domin magance matsalolin da yawan barace baracen ke haifar wa a tsakanin al'ummar jihar. Matakin ya nuna cewa hakan zai kawo karshen duk wani yawace yawacen da mabarata a fadin jihar ke yi tare da tantance wadanda ke da bukatar agajin gwamnati dan iya dogaro da kai.
Sai dai rahoton ya bayyana cewa akwai wani shiri da gwamnatin ke kokarin yi don yi wa almajirai tanadi, da kuma saukaka masu samun damar samun abincin yau da kullum.
Gwamnatin jihar dai tace wannan matsala ta barace barace babbar matsala ce da ke neman agajin gaggawa, kuma za ta yi duk mai yiwuwa don taimakon mabaratan da kuma basu damar dogaro da kai.
Title :
Za A Hana Bara A Jihar Zamfara
Description : Daga zuma times hausa Wani rahoto da ke fitowa daga Gusau fadar gwamnatin jihar Zamfara ya na nuni da cewa, shiryen shirye sun kankama na k...
Rating :
5