Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara aikin hako danyen man fetur a jihar Bauchi.
A wani bayani ga manema labarai da ya fito daga ofishin Mataimakin Gwamnan Bauchi kan Sadarwa Shamsudeen Lukman Abubakar ya ce, Babban Darekta na Hukumar NNPC, Dakta Maikanti Kacalla Baru ne ya bayyana haka a yayin da ya ziyarci Gwamnan jihar Bauchi Mohammad Abubakar a ofishinsa.
Babban Darektan ya ci gaba da cewa yana da kyakkyawan zaton cewa za a samu albarkatun danyen man fetur mai tasiri a jihar in an yi la'ankari da yadda jiyar ke makwaftaka da tafkin Chadi da ingantattun na'urorin zamani da ake amfani da su don gano man din.
Dakta Baru ya kara da cewa tuni NNPC ya bude sashin na musamman a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da Jami'ar Modibbo Adama da ke Yola domin ba da horo na musamman don ganin cewa aikin zai bunkasa tattalin arzikin jihar kana zai samar da ayyukan yi da dama ga matasa.
Dakta Baru ya yabawa wa gwamnan bisa goyon bayan da ya ke bai wa kamfanin na NNPC wajen ganin aikin hako man ya kankama inda
ya ce hakan yana daya daga cikin dalilan ziyarar don nuna godiyarsa.
Gwamnan Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammad Buhari don kokarinsa na gani an samu Man Fetur a Jihar.
Ya kuma jinjina wa NNPC a karkashin jagorancin Dakta Badeh don kokarin hako man a Bauchi inda ya bayyana kokarin da gwamnatinsa ke yi na ganin an bunkasa sauran fannonin da suka hada da noma da kiwo, masana'antu da kawata gandun jihar don masu zuwa yawon bude ido.
source Zuma Times Hausa
Title :
Za A Fara Hakon Danyen Mai Fetur A Bauchi
Description : Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara aikin hako danyen man fetur a jihar Bauchi. A wani bayani ga manema labarai da ya ...
Rating :
5