** Farida takanyi takaici akan duk wani abin
farin ciki da zai samu y'ar amana, haka
kuma takanyi farin ciki akan duk wata
kaddara ko masifa data afka mata.
Ko kadan a zcyrt bata yarda cewa Y'AN
UWAN JUNA suke ba, hakan yasa bata kllnta
a matsayin yar uwa.
Gefe guda kuma fifikon son da mahaifinsu
ke nunawa nusaiba (Y'AR AMANA) ke kara
rura wutar kiyayya mafi girma a zcyr farida,
domin tana ganin kmr ita kadai ya ware
baya kaunarta.
Bama shi kawai ba a ganinta duk sauran
mutane ma sunfi kaunar nusaiba akanta
idan ka cire mominsu, duk inda sukai sunan
y'ar amana ake kira sbd kowa da ita yake
son yayi mu'amala.
Harta a makarantartasu sunan Y'AR AMANA
ya zagaye ko'ina ciki da waje dalibai da
malamai kuma maza da mata, wanda dalilan
hakan nada ma2kar yawan gaske!!
Kololuwar Kokari da fahimta, iya mu'amala
da girmama mutane, sanin daraja da kimar
dan adam gami da rashin girman kai
sabanin farida da bata dauki koda 20% na
kyawawan halayen nusaiba ba ga
tsagwaron grmn kai da gadara wanda ya
kara sawa sam jama'a basa sha'awar
mu'amala da ita.
Sai dai ko kadan hnklnta bai taba kawo
cewar halayenta ne abin gudu ba, a rashin
hnklnta mutane na kinta ne sbd nusaiba
don haka muddin suna tare tofa ita
haskenta bazai taba bayyana ba.
Bbn burinta kuma abinda take so shine
fallasuwar wani sirri dazai tbbtr mata cewa
nusaiba ba yar gdnsu bace, hasashenta
kenan a kllm.
Don me abba zai rinka kiranta Y'AR AMANA??
Y'ar riko fa kenan.
Farida kanyi duk sanda tayi irin wannan
tunanin....
*Kmr kllm sai byn azahar suka dawo, a hnkl
motar tasu samfurin kyau da kawatuwa ta
karyo kwanar hamshakiyar unguwar tasu
me kyaun tsari da kayataccen zubi. Kll daya
zaka yiwa motar kasan y'ay'an gata ne a
cknta, rufe take da bakin tintek ta yadda
ba'a iya ganin wanda ke ciki.
A hnkl ta tsaya worn daya aka doka tafkeken
gate din gdn ya fara budewa jim kadan
motar ta zarce izuwa ckn harabar gdn
tsakiyar sauran tsala-tsalan motocin alfarma
dake ciki, a tare kofofin motocin suka bude
farida ta fito ta bangaren hagu yayinda
nusaiba ta fito ta bangaren dama.
Kll daya zakayi musu dukkansu kasan akwai
gajiya ma2ka a tare dasu, a tare suka taka
tare da wucewa izuwa ckn gdn sai dai ba
wata hira dake gudana tsakaninsu koda
kuwa ta i da a'a ce. Zaune suka tarar da
mominsu a falon jin motsinsu yasa ta dago
kai tare da duban farida tace "kun dawo??".
Mun dawo momi.
Y'ar amana ta amsa ckn kayatacciyar
muryarta.
Ke aka tambaya??
Farida ta fada tana me dubanta,
"munafuncin banza kawai da kika saba."
ta karasa zancen tare da karasawa kujerar
da momi ke zaune ta zauna ckn shagwaba
tace "mun dawo momi..." ba tare da momin
ta kula da nusaiba dake tsaye ba domin ta
saba nuna tsantsar rashin kulawa a gareta
da kuma nuna mafificin fifikon soyayya ga
Y'AR GABAN GOSHInta kmr yadda take kiran
farida. ta jawo hannun farida tare da cewa
"to sannu da dawowa y'ata ta gaban
goshina."
Kai! amma fa na kwaso gajiya da yawa
momi, sai kace anyi min duka wlh.
Ta sake fada. Momi ta bita da kll irin na
tausayawa tace "ashsha! Amma ai kin dawo
gida yanzu hutu sai irin wanda kika zaba, ko
goyaki kike so inyi ai ba damuwa."
farida tayi saurin dago kai da cewa "kai! Duk
girmana??"
dukkansu sukai dariya a tare.
*nusaiba dake tsaye a hnkl ta taka tare da
wucewa izuwa dakinsu, tana shiga ta mayar
da kofar ta rufe dai-dai lkcn zcyrta tace mata
"a haka zan tbbt har abada bansan dadin
uwa ba kenan??
Bata kaunata ko nuna kulawa a gareni, anya
kuwa momi da nake kira mahaifiyata ita
dince da gaske kuwa??"
tabi jikin kofar tare da daga kanta sama
wanda ya baiwa hawayen idonta damar
gangarowa izuwa kuma2nta, jim kadan ta
gogesu tare da karasawa ckn dakin sbd
bata fiye barin damuwa a zcyrt tayi tasiri na
tsawon lkc ba. Ktwr jakar dake hnnnta ta
ajiye a gefen makeken gadon, ta zarce tare
da dauro alwala ta dawo tare da jawo
darduma ta tada sallah.
Y'AR AMANA kuma BAIWAR ALLAH ta gaske
kenan, bawai nutsuwar sallar tata kawai ne
abin sha'awa ba, gama sallar tata keda wuya
ta jawo alqur'ani me girma ta fara
karantawa kasa-kasa kuma ana jiyo sautin
da daddadar muryarta, har sai da aka kira
sallar la'asar ta mike ta kawota tayi addu'o'i
data saba ta mike tare da cire katon hijabin
data saka tayo waje izuwa falon gdn.
**Zaune a kytccn falon samfurin alfarma
zaune suke su biyu, farida ce da wata
kawarta me suna hadiza wacce tazo ba
dadewa. Kwararriyar magulmaciya ce hakan
yasa 2nda suka fara hirar munafuncin
nusaiba da zundenta kawai suke, sukanyi
dariya harda tafawa idan ta kama.
Jin motsin tawowarta yasa suka dakata da
maganar da suke yi, farida ta rankwafo da
kanta ckn rada tace "kunyi sallah kuwa??
Bari kiji abnd munafukar zata fada kenan."
a hnkl ta fito daga dakin ta saki fara'arta
data saba a duk sanda taga wani bakon,
tace "hadiza ce yau a gdn namu?? Sannu da
zuwa.
Uhm! Yauwa. Ta fada tana me tabe baki.
Harta wuce ga inda ta nufa sai kuma ta
dakata tare da juyowa tace "Ah! Lokacin
sallah yayi fa 2n dazu."
farida ta kaso kunne tare da cewa "me kika
ce?? Ke muryarki ba wani karfi ba kuma ki
rinka magana ciki-ciki."
cewa nayi "kunyi sallah kuwa?? Lkc yayi fa!"
farida da hadiza suka kyalkyale da dariya
harda tafawa, "bana gaya miki ba??" ta fada
tana duban kawartata ta juyo ga nusaiba
tace "Tasallah kenan sarauniyar ibada to
mun ji kuma mun gode."
farida ta fada har yanzu dariyar sukeyi.
Nusaiba tabisu da kallo kawai tayi kokarin
danne takaicin daya mamaye zcyrta ba tare
daya fito fili ba kada su sami yadda suke so
ta zarce izuwa kitchen domin dama can ta
nufa.
** sai data dauki tsawon lkc a tsaye tana
tunani da nazarin abinda ya faru, Sai dai duk
nisa da zurfin da 2nanin nata yayi ta kasa
tuno ko gano dalilin da yasa farida ta riki
wulakantata a matsayin wani abu daya
zame mata dole a kllm.
.....Ta sake tattara tunanin ta watsar a karo
na biyu tare da 2nkarar abinda tazo yi,
abinci ta zuba a plate dai-dai da bukatarta ta
juya ta fice dauke farantin ba tare data sake
duban inda suke ba ta wuce daki.
** Misalin karfe bakwai da y'an min2na na
dare bayan sallar magriba ba jimawa kenan,
zaune a kayataccen falon alfarmar su uku ne
rak! Kowanne daga cknsu mazauninsa
daban babu kuma me yiwa wani magana
saima harkar gbnsu da kowa keyi, mominsu
idonta nakan akwatin television dake
manne a jikin bango gaba daya hnklnta ya
tafi ga abnd take kll.
Farida kuwa zaune take bisa kujera tayi
zaman isa da gadara idonta nakan dan
gajeren novel dake hannunta tana
karantawa, kll daya zakayi mata kasan tana
ma2kar jin dadin ynyn da take ciki.
Sai kuma nusaiba dake can gefe zaune
kawai ba komai a hnnta kuma ba abnd ta
mayar da hnkl gareshi, Zuwa can ta dago kai
tare da cewa "farida".
Ta kira sunan nata don jawo hnklnta. Ba
tare da faridan ta dago kai ba tace
"nusaiba".
Kinko lura yau Abba ya wuce lkcn
dawowarsa??
Mominsu dake can zaune ta juyo tare da
fadin "ko kina 2nanin ya bata ne mu tashi
mu tafi cigiya??"
da sauri ta grgz kai da fadin a'ah momi ba
haka nake nufi ba...
Toh! Zai dawo mana sau nawa yana wuce
iwar hkn??
Momin ta fada tare da mayar da kanta ga
abnd take kll.
Farida ta yatsina fuska da cewa "tsabagen
kalon zancen tsiya ne kawai irin nata."
sallamar akayi direban gdn ya shigo tare da
risinawa ga momi wacce a dai-dai lkcn ke ce
masa "ka tafi ga aiken nan da nayi maka
dare fa nayi."
to hajiya. Ya amsa tare da zartowa inda nake
ya miko min dukkan mukullan hannunsa,
nabishi da kll kawai tare da cewa "na meye
wadannan??"
Alhaji ne yace duk sanda zan fita na baki
mukullan duk motocin gdnnn ki ajiye har sai
na dawo.
Momi da farida sukayi saurin duban juna
ckn mamaki, shine ya fada maka hakan da
kansa??
Momi ta tambaya tana dubansa.
Da gyada kai yace "kwarai shi ya fada min
haka."
Ta gyada kai ckn takaici tare da cewa "lallai!
Abin nasa babba ne, wuce to aiken naka ma
an fasa."
da sauri ya juya don da alama abnd yake so
kenan.
Har yanzu idonsu na kan nusaiba tamkar
wacce tayi musu wani bbn laifi, momi ta
sake gyada kai tace "toke saiki shirya don
ina jin nan gaba abinda zamu ci ma sai kin
bada izini za'a bamu a gdnn."
ga dukkan alamu hkn na gab da faruwa.
Farida ta karawa zancen karfi.
Nusaiba binsu da kll kawai take ba tare da
tace komai ba.
Jim kadan Abban nasu ya dawo da
sallamarsa ya shigo dukkansu suka amsa
tare dayi masa barka da dawowa, sai a
yanzu ne nusaiba ta samu nutsuwa da
karfin gwiwa sosai domin gatan nata ya
dawo me share mata hawaye.
Sun dan taba hira dashi kadan zuwa jimawa
ya mike tare da jawo jkrsa ya mike zai nufi
dakinsa har ya taka sai kuma ya dakata tare
da duban nusaiba yace "Y'AR AMANA yadai
koda wani abune??
Wannan klln da dalili..."
Abba dama... Dama wani littafi nake son siya
don yin nazarinsa akwai amfanin dazai
yimin ma2ka."
shine kawai dama kike ta noke-noke?? A
hnkl ya zira hannu ckn aljihun rigarsa tare
da zaro kudi masu yawa ba kuma tare da
dubawa ba ya mika mata, ckn ladabi ta amsa
tare da cewa "kai! Abba sunyi yawa ai".
Ki siya sauran sai kiyi wani amfanin dasu.
Koda farida ta kyalla ido sai kuwa tayi saurin
cewa "Abba nifa?? Nima fa ina da bukatar
kudin nan kawaici kawai nayi amma sai naji
shiru??"
ya juyo gareta yace "bani da kudin baki ka
sayi NOVEL na banza mara amfani, ki bari sai
kin bukaci abu me muhimmanci sai kizo ki
amsa."
yaja jakarsa tare da wucewa izuwa dakin
nasa. Farida tabishi da kll kawai kmr ta fashe
da kuka don takaici, ta saki novel din dake
hannunta ya fadi kasa, tace "kin gani ko
momi??"
kafin tayi magana nusaiba tace "karki damu
sister bari mu raba."
farida ta dubeta ta doka tsaki ta mike tabar
falon sbd bakin ciki. Ta barsu su biyu jal a
falon.
**Irin abubuwan dake kaiwa da komowa a
ckn gdn kenan, ta yadda zaka rasa gane kan
abin ko kuma bakin zaren dake da wuyar
ganuwa, uwa tadau bangaren da soyayyarta
tafi karkata sannan uba ma ya dauki nashi
bangaren. Tambayar anan ita ce ko meye
dalilin wanzuwar hakan?? Dole idan aka
koma can kasan tarihi za'a iya tono sirrin.
** BAYAN KWANAKI UKU **
motar su kirar toyota highlander ce bisa
kwalta ke sharara gudu byn dawowarsu
daga mkrnt kmr yanda suka saba, misalin
1:40 na rana sanda motoci keta kaiwa da
kawowa.
Yar amana dake zaune ta dubi direban tace
"pls mubi ta SDK BOOKSHOP zanse wasu text
books daga can sai mu wuce..."
caraf farida ta grgz kai tace "bazai yiwu ki
tsaida mu ba ki bari a kaini idan yaso sai ki
dawo ki shekara ma, kai mu tafi gd kai
tsaye."
To a tsaya na sauka ni na dawo a motar
haya don dole sai na sayi lttfnn yau. Nusaiba
ta fada.
Na saukeki?? Rufan asiri!! Kiyi hkr farida
gsky dole mu tsaya a inda yar amana keso.
Haka kuwa akai a dai-dai katafaren shagon
suka tsaya ta fita ta tsallaka ta shiga, tadau
tsawon lkc a ciki kafin ta fito dauke da leda
me dauke lttffn data siyo, dai-dai lkcn bisa
kskr wanda yazo shiga hnnsa ya bigi ledar
ta fadi kasa lttfn suka watse tayi saurin dago
kai suka hada ido tabishi da klln don tbbs ta
ganeshi, karo na biyu kenan da abbw biyu
masu kama da juna suka faru tsknnta dashi.
Ba zata taba manta fuskarsa ba, bare
sunansa daya fada mata da kansa ba....
To waye wannan?????
Title :
Yar Amana Part 4
Description : ** Farida takanyi takaici akan duk wani abin farin ciki da zai samu y'ar amana, haka kuma takanyi farin ciki akan duk wata kaddar...
Rating :
5