'
Kungiyar 'yan uwa musulmi a Nigeria ta maida martani kan
harmata kungiyar da gwamunatin jihar Kaduna ta yi.
Kungiyar ta 'yan Shi'a ta ce haramcin da kaka yi mata ya saba
ka'ida.
Mai magana da yawun kungiyar Malam Ibrahim Musa ya ce za su kaluabalanci wannan mataki na gwamnatin ta Kaduna.
"Muna Allah wadai da wannan matakin da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka, ba mu yarda da shi ba, za mu kalubalance shi ta dukkan hanyar Amma ya ce matakin bai basu mamaki ba, ganin irin take-taken hukumomin na Najeriya dangane da kungiyar.
Kakakin na 'yan shi'a yace duk abin da su ke yi bai saba dokokin Najeriaya ba.
A wata sanarwa da ta fitar ne dai ranar Juma'a gwamnatin ta jahar Kaduna ta ce ta soke wannan kungiya, haka kuma ta haramta dukkan ayyukan ta a dukkan fadin jahar.
Mai magana da yawun gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufa'i, ya ce za a daure duk wanda aka samu yana aiki a matsayin dan
kungiyar, tsawon shekaru bakwai a gidan yari.
Samuel Aruwan ya ce gwamnati ta dauki matakin ne, ta yin amfani da karfin da tsarin mulki ya bata, domin tabbatar da tsaro, da bin doka da oda, da zaman lafiya a jihar.
Daruruwan mutane ne suka mutu lokacin da aka yi arangama a watan Disamba tsakanin 'yan kungiyar da sojojin Najeriya bayan
sojin sun yi zargin cewa 'yan Shi'a sun yi yunkurin halaka shugabansu, Laftanar Janar Yusuf Buratai.
Sai dai 'yan kungiyar sun musanta zargin, suna masu cewa sojoji sun kashe dubban mabiyansu.
Hukumomi na > da shugaban kungiyar Sheikh Ibraheem Zakzaky tun watan Disamba.
Title :
Yan Shi'a Sun Mayar Da Martani Kan Haramci
Description : ' Kungiyar 'yan uwa musulmi a Nigeria ta maida martani kan harmata kungiyar da gwamunatin jihar Kaduna ta yi. Kungiyar ta 'ya...
Rating :
5