A sanyin safiyar yau Asabar ne al'ummar yankin makarantar 'School of Nursing' dake garin Maiduguri babban birnin jihar Borno suka wayi gari a ganin wani barawon wuta da ya makale a jikin na'urar wuta ta tiransifoma a yayin da suka shiga cikin domin su yi sata.
Rahotanni sun nuna cewa matasa uku ne suka je satar amma da suka ga tiramsifomar ta makale dan uwan nasu sai suka guda suka bar shi.
Majiyarmu ta gano cewa matashin ya kai kusan tsawon awanni uku a makale a jikin na'urar tiransifoma daga bisani ta sake shi ya fado amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto yana raye bai mutu ba. Saidai fatar cikinsa ta sabule.
Madogora Rariya
Title :
Wutar Lantarki Ta Rike Wani Barawo Da Ya Je Sata A Cikin Na'urar Wuta Ta Tiransifoma
Description : A sanyin safiyar yau Asabar ne al'ummar yankin makarantar 'School of Nursing' dake garin Maiduguri babban birnin jihar Borno su...
Rating :
5