Hukumar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta Kama wata mata ‘yar shekara 51, Rose Edward wadda ake zargi da sayen jariri dan wata biyu kan kudi N450,000, cewar NAN. Rohotannin na nuna ‘yan sanda sun kuma kama wani likitan gargajiya Eneyo Nyang da kuma uwar jinjirin Comfort Effiomg saboda hannu da suke dashi cikin aikata laifin
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Akwa Ibom, Murtala Mani, ya gaya ma masu daukar labarai ranar Assabar 22 ga Oktoba a garin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom
Mani, ya fadi haka ta bakin kakakin hukumar ‘yan sanda na jihar, mukaddashin suprtanda Cordelia Nwanwe,yace Edward daga jihar Rivers ta amsa sayen jaririn domin tana bukatar jinjirin kanta. Uwar jaririn, Comfort Effiong ta amsa sayar da jaririn domin bata da mai kulawa da ita.
Tace wanda na sayar da jaririn saboda taimako. Bani da mai taimako na, ubana ya mutu, uwata bata da lafiya, kuma bani da mai taimako na.
Title :
Wata Uwa Matashiya Ta Saida Jariri Akan N450,000
Description : Hukumar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta Kama wata mata ‘yar shekara 51, Rose Edward wadda ake zargi da sayen jariri dan wata biyu kan kudi N4...
Rating :
5