Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun yi tir da kalaman da Nafisa Abdullahi ta rubuta a shafinta na Instagram cewa ba ta da wata alaka ta kawance ko ‘yan uwantaka da Rahama Sadau.
Nafisa ta bayyana haka ne bayan wasu sun yi ta kiraye-kiraye a gare ta da ta tsoma baki domin a janye korar da aka yi wa Rahama daga harkar fina-finan Hausa bayan an same ta da laifin rungumar mawaki Classiq a wani bidiyo da ya fitar.
Jarumar Kannywood, Ummi Ibrahim, wacce aka fi sani da suna Zee Zee ta yi wa Nafisa raddin cewa abin da ta yi bai kamata ba.
A cewarta, “Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne; ko ba kwa shiri da ita bai kamata ki nunawa duniya ba, don wannan rubutun da kika yi wani zai yi zaton ba kya son (Rahama) ne”.
Zee Zee ta kara da cewa matsalar da ta shafi Rahama ta shafi dukkan masu yin fina-finan Kannywood domin kuwa idan abin zagi ta yi dukkan su za a zaga ba ita kadai ba.
‘Kowa ta kansa yake yi’
Ita dai Nafisa Abdullahi ta yi ikirarin kowa ta kansa yake yi tsakanin ‘yan kannywood, tana mai cewa lokacin da wani ya wallafa hotonta sanye da gajeren wando—batun da ya janyo mata zage-zage—babu wata ‘yar Kannywood da ta fito ta kare ta duk da yake sun san cewa an yi ne domin a bata mata suna.
A cewarta, “Ina mamakin yadda masu amfani da shafin Instagram ke daukar mu [‘yan fim] wallahi. Ya kamata ku sani cewa da ni da Rahama sana’armu guda, amma babu abokantaka ko ‘yan uwantaka tsakanimu. Kai, babu wata dangantaka tsakaninmu mata ‘yan fim. Don haka, duk wanda yake tunanin muna jituwa yaudarar kansa kawai yake yi.”
Ta kara da cewa ta yi amanna Rahama za ta iya jure wa halin da ta fada a ciki, sannan ta yi kira ga mutanen da ke son ta bi sahun masu kiraye-kirayen a janye korar da aka yi wa Rahama su daina bata lokacinsu.
Title :
Wasu ‘Yan Fim Sun Yi Tir Da Nafisa Abdullahi Kan Rahama Sadau
Description : Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun yi tir da kalaman da Nafisa Abdullahi ta rubuta a shafinta na Instagram cewa ba ta da wata alaka ta ka...
Rating :
5