Babban Magatakardan Kungiyar Izala ta kasa Sheikh Muhammadu Kabiru Gombe ya ja hankalin Al’ummar kasa kan Godewa Allah a Kowanne irin yanayi. Shehin malamin da yake gabatar da jawabi a wani taron wa’azin Musulunci a Victoria Island dake birnin Legas a ranar talata, ya bayyana muhimmancin godiya ga Allah Madaukakin Sarki a duk halin da al-ummah ta samu kanta a ciki. Haka zalika ya danganta matsalolin da kasar ta shiga ciki a matsayin sashi daga cikin laifukan da al’umma ke yi na rashin duba ni’imomi da Allah Ya yi mata.
“Nijeriya Allah Ya yi mana Ni’ma. Kun san Ni’imar da Ya yi mana. Zuwan mulkin wannan shugaban (Buhari) Ni’ima ce. Mu muka san bala’in da muka gani da idanun mu. Dahuwa da suya duk labarin wuta suke ji, amma gashi shi ya ga wuta tsirara. To mu mun gan ta tsirara, mu muka san bala’in da muka gani. Dazu na ke magana da wani Yaro da ya kira ni a waya ina cikin Legas ɗin nan, rabon da na ji muryarsa shekara biyu kenan. A Bama ya ke. Na ce kana nan da rai? Ya ce ina nan amma an kashe ƙanina. Nima an kawo hari a kashe ni na tsallake. Na ce ina Mahaifiyarka? Labarin da ya riƙa ba ni idan ka ji za ka zubar da hawaye. Na ce yanzu kana ina? Ya ce ya yi gudun hijira amma ya dawo. Ya ce yanzu an fara gina musu gidaje na bakin hanya kuma an ce duk za a gina musu. Baga ta zama makabarta yanzu an dawo ana gina ta. Ka je sansanonin yan gudun hijira, mun yi magana da Barista Nafi’u (Sakatare na Spring Council For Shari’a) ya ce akwai Marayu kusan Miliyan daya. Da wancan bala’in ya wuce har zuwa yanzu, daga Kaduna har ka dangana da Maiduguri babu sauran dan Adam a wajen. Ni’ima ce. Yau wannan abu ya zama tarihi. Bama wannan ba tun da kuke kun taɓa ji an kama alkali? Na babbar kotu? To yau guda nawa aka kama? A baya idan aka ce maka Nijeriya za ta zama haka, za ka yarda? Wallahi wannan mulkin Rahama ne. Ni’ima ce. Ko ka samu kudi ko ba ka samu ba. Wannan Ni’ima ce babba da Allah Ya yi mana”.
Title :
Wallahi Mulkin Buhari Ni’ima Ce Ga Nijeriya – Kabir Gombe
Description : Babban Magatakardan Kungiyar Izala ta kasa Sheikh Muhammadu Kabiru Gombe ya ja hankalin Al’ummar kasa kan Godewa Allah a Kowanne irin yanay...
Rating :
5