Dalili da cece-kuce da ake ta yi don wani odiyo na wata mata, Aisha Anka, da ke ta yawo a yana gizo inda wasu suka yi zargin cewa ƙungiyar Izala ce da haɗin bakin gwamnati ke da alhakin wannan safara ta wa'yannan mata zuwa Saudiyya.
Zuma Times Hausa a ƙoƙarinta na gano ainihin gaskiyar al'amarin, wakilanta sun yi tattaki.zuwa ofishin ƙungiyar Izala da ke Abuja inda shugabar Kamfani, Mairo Muhammad Mudi ta tattauna da Malam Muhammad Kabiru Gombe, sanannen mai wa'azi kuma Sakataren Ƙungiyar kan wannan al'amari da wasu matsaloli da dama da suka shafi Musulmi Arewa tumma matasa.
A yi karatu lafiya.
ZT-Menene alaƙar ƙungiyar Izala da wani zargi da wasu mata a audiyo da ke ta yawo a yanar gizo inda suka dangata ƙungiyar da zargin da wata, Aisha Anka ta yi inda ta ke kukar cewa an yaudare su aka kai su Saudiyya da nufin za su yi wa Musulunci hidima amma sai ga shi ta ce a ɗora su bisa bauta?
Malam Kabiru Gombe- Babu shakka wannan audiyo da kike faɗa, ni ma na ji wata mata ta ke ta rusa kuka cewa wasu kamfani suka ɗauke ta suka kai ta Saudiyya da cewa za ta yi shara a ɗakin Ka'abah, ta yi shara a masallacin Annabi sannan ta yi wa alhazai abinci amma daga ƙarshe a kai mai da ita baiwa inda ta ce ba ita kaɗai ba ne suna nan da dama aka rinƙa haɗa su da aiki kuma ba abinci sannan ana ta azabtar da su. Kuma babu shakka na ji wasu suna danganta wannan da ƙungiyar Jama'atul Izalatul Bidi'a Wa Iƙamatus Sunna musamman shugaban kungiyar na ƙasa Sheik Abdullahi Bala Lau.
Wani abun ban tausayi ma wasu har da sunan addini suka rinƙa irin wannan maganar har da wasu jagororin addinin suma suna irin wannan zargi saboda kila saboda wasu dalili nasu da ba za su iya fitowa da su ba sai suka bi ta wannan hanyar.
To kin ga Allah Ya wanke mu kafin mu wanke kanmu don akwai wani kamfani mai suna Traveling Express Limited waɗanda suka fito suka ce su ke da alhakin ɗauko waɗannan mata kuma sun ƙaryata zancenta akan cewa sun riga sun faɗa mata ainiyin abinda za ta je can ta yi wanda da kanta ta saka hannu cewa za ta yi 'husemaid' watau aikatau.
To ko ma wanene ke da gaskiya a tsakanin matar da kamfani ba shi ke da muhimmaci ba a nan abinda ni ke son ki gane shine Ƙungiyar Izala ba ta da alaƙa da wannan, Izala ba ta taɓa ƙulla wata yarjejeniya da wani kamfani a Saudiyya ko a nan Nijeriya da sunan ɗaukar mata a kai su Saudiyya a mai da su bayi a can ba. Izala ba ta cikin wannan, babu wata takarda da ta taɓa sa wa hannu cewa ta ɗauki wata mata ta kai can. Wasu kamfanoni ne suka yi harkarsu can tare da wasu mata suka samu matsala can wanda ba mu da masaniya sam.
Hanya ɗaya mu ke bi kan maganar aikin yi, ita ce ta Manara Jobs watau hanyar samo da aiki na ƙungiyar ta Izala.
ZT: Malam ka mana bayani kan tsarinku na Manara Job.
Malam Kabiru Gombe: Manara job shine tsarin da mu ke da shi na samo wa 'ya'yan talakawa ko marayu aiyukan yi, za ka iya ganin ɗan talaka ko maraya yayi digiri ko difiloma amma bai da hanyar da zai iya bi ya samu aiki a gwamnati, to wannan tsarin zai iya bi don ganin slan samo masa aiki da wasu kamarsa wasu jagororin addinin suma suna irin wannan zargi saboda kila wasi dalili na su da ba za su iya fitowa da shi ba sai suka bi ta wannan hanyar.
To kin ga Allah Ya wanke mu kafin mu wanke kanmu don akwai wani kamfani mai suna Traveling Express Limited waɗanda suka ce su ke da alhakin ɗauko waɗannan mata kuma sun ƙaryata zancenta akan sun riga sun faɗa mata ainiyin abinda za ta je can ta yi wanda da kanta ta saka hannu cewa za ta yi 'husemaid' watau aikatau.
To ko ma wanene ke da gaskiya a tsakanin matar da kamfani ba shi ke da muhimmaci ba a nan abinda ni ke son ki gane shine Ƙungiyar Izala ba ta da alaƙa da wannan, Izala ba ta taɓa ƙulla wata yarjejeniya da wani kamfani a Saudiyya ko a nan Nijeriya da sunan ɗaukar mata a kai su Saidiyya a mai da su bayi a can ba. Izala ba ta cikin wannan, babu wata takarda da taɓa sa wa hannu cewa ta ɗauki wata mata ta kai can. Wasu kamfanoni ne suka yi harkarsu can tare da wasu mata suka samu matsala can wanda ba mu da masaniya sam.
ZT: Malam ka yi bayani kan tsarinku na Manara Job.
Malam Kabiru Gombe: Manara job shine tsarin da mu ke da shi na damo wa 'ya'yan talakawa ko marayu aiyukan yi, za ka iya ganin ɗan talaka ko maraya yayi digiri ko difiloma amma bai da hanyar da zai iya bi ya samu aiki a gwamnati, to wannan tsarin zai iya bi don ganin ya samu aikin yi kamar yadda muke da tsarin ɗaukar nauyin karatun waɗanda ke ɓukata.
Amma maganar ɗaukar mata zuwa wani wurin don aiki Izala ba ta da alaƙa da wannan alaƙar ta kusa ko ta nesa. Banda wannan Izala ƙungiya ce da ta ka yi wa'azi na addinin Musulunci, ƙungiya ce da ta ke koyar da sunna ta Annabi Muhammad ﷺ Sallalahu Alaihi Wa Salaam. Kuma duk lokacin da za ka karantar da irin karantawar Manzo ﷺ Sallahu alaihi wa salaam to za ka haɗu da jarabawa da dama kamar yadda Shi Manzo ﷺ Ya fuskanta a wajen maƙiya.
Ganin cewa ƙungiyarku ta addini ce da magoya baya da dama kamar yadda ka faɗa a baya cewa ba za a rasa maƙiya da za su iya amfani da irin waɗannan yanayi don ɓata sunanku ba, to me zai hana in kun samu irin wannan koke ko kun ji, ku yi bincike ko don a taimaka wa waɗannan mata in da gaske ne sun shiga wannan hali?
Malam Kabiru Gombe- A gaskiya da kamar a ce wai wannan matar ko masu irin wannan matsalar tun farko sun tuntuɓe mu, muna da ofisoshinmu a ko'ina a ƙasar nan, da mun shiga cikin maganar mun gano ainihin gaskiyar don taimaka masu fita daga cikin wannan ƙunci. To amma ta ina za mu fara, ba mu san ma inda ta ke ba, muryarta kaɗai aka ji tana kuka sai wani mutum da ya tambaye ta shi kuma ko suna ba a sani to ta ina za a bi a taimaka masu? Amma in har yau za mu samu matar nan, In Shaa Allah za mu sa baki mu ga ba a cuce su ko addini ba
Izala ƙungiya ce ba gwamnati ba, ko kotu ce dole sai an kai mata ƙara tukun za ta saurara. A shirye muke mu saurari irin waɗannan ƙorafi sai mu bi hukumomin da suka dace don warware matsalar.
ZT: Zancen muharram, kowa shaida ne a lokacin da 'yan Nijeriya mata suka tafi Saudiyya babu muharramansu, an dawo da su, ibada zasu tafi, bai wuce na mako biyar zuwa shida ba. Amma yau sai ga shi wannan tafiya da su yi na aikatau, na tsawon shekaru biyu, kamar yadda wannan jami'in ya fada, kowanne daga cikin matan ba su kasa shekaru 40 ba, amma akan amince su tafi.
A ba mu fatawa Malam tunda wa'yancan mata ibada za su tafi, amma aka ce ba a yarda su tafi babu muharrami ba, amma sai gashi an yarda su waɗannan su tafi har na zaman shekaru biyu babu muharrami.
Malam Kabiru Gombe: Ban san menene dalilan wannan kamfani, ko kuwa ka'idar da gwamnatin Saudiyya ta dogara da ita ba ko ma gwamnatin Saudiyyar na da masaniya dangane da wannan irin abubuwan da suke yi ko bada saninta da amincewarta suke yi ba duk ban sani ba In kuma da saninta da amincewarta, wani dalilai ne suka dogara da su na bawa waɗannan mata dama na ɗauko su a kawo su domin irin waɗannan aiki.
Ko dai da ban san komai akan wannan ba, amma kamar yadda kika ce menene fahimta ta akan haka,m. Abunda zan iya fahimta a nan shine, kamin a yi ma wannan maganar, ta wannan kamfanin da suke daukar mata zuwa wannan aiki, a yanzu haka da muke wannan maganar da ke, akwai matan nan su ke Saudiya ɗin, waɗanda yawancinsu 'yan Nijeriya ne da ma maza ba mata kaɗai ba, har ma akwai waɗanda ba ' yan Nijeriya ba ne Hausawa ne daga cikin ƙasashe da muke makwabtaka da su amma dukkansu ana musu kallon 'yan Nijeriya saboda girmar, kimanta da bunkasarta da kuma karfinta a ƙasashen duniya.
To suna nan a kasar suna zaune ba tare da izinin Saudiyya ba, ba ma shekara biyu da su wadannan kamfani suke kwangila da wadannn mata ba, wata ma a can aka haife ta, kuma uwar nata ta je ne ba tare da izinin irin wannan zama ba sai ta haife ta. Kuma duk wanda yake zuwa aikin Hajji da Umura, ya san irin waɗannan matan da muke magana akai, kina iya samun wasu daga cikinsu dama tun a nan Nijeriya kafin su tafi can, ba sanmnin addini suka yi ba, can kuma daman ba sun je domin koyan addini ba ne, sun je ne domin neman kudi ne. Saboda haka duk harkar da za su shiga suga sun kwana lafiya, to mafi yawa daga cikinsu zasu iya shiga ciki domin suga sun sami kuɗi.
Wannan matsala ce wadda ko ita gwamnatin Saudiyya tana fama da ita, ba ma gwamnatin Saudiyya kaɗai ba, mu kanmu a 'yan Nijeriya kuma jagororin addini a nan Nijeriya, wannan mtsalar tana ɗaya daga cikin matsaloli da ke damun mu. Mun sha mu je har ofishin Jakada na Nijeriya da ke Jidda, mun tattauna da shi na menene ya kamata ya kawo karshen wannan matsala.
Har yanzu Saudiyya ba ta yarda da waɗannan mutanen 'yan Saudiyya ba ne, suna zama ne babu izini, suna guje-guje ne da jami'an tsaro, suna kwana akan unguwanni da ke kan tsaunuka da tuddai. Ba su zauna cikin kwanciyar hankali ba, su ba gwamnatin ta ba su damar zama ba, ba ta basu damar karatu a kasarta ba, ma fi yawa da sun samu sun yi makarantar firamari, sun yi sakandare shikenan ba za su samu daman yin jami'a ba.
Mace da aka bar ta tana rayuwa babu ilimi, ba za a san irin bala'in da za ta saka kanta da wadanda suke zama tare da ita ba. Yana ɗayq daga cikin dalilin da ya sa Kungiyar jama'atul Izalatul Bidi'a wa'ikamatus Sunnah muka mai da shi, duk shekara idan muka je muna zagaya irin waɗsnnan unguwannin Hausawa, a Makka muna ci gaba da yi musu wa'azi, kuma alhamdulilah, muna yi wa Allah godiya, muna samun ci gaba ƙwarai dangane da addini kuma suna komawa tafarkin Allah. Muna bin masallatai daban-daban da ke cikin Makka muna yin wa'azi.
Bamu tsaya nan ba, yana daga cikin dalilin da yasa muka bude gidan talabijin na Manara kuma muka ɗorata akan Nilsat Afrika, muka sake ɗora ta akan Gabas ta Tsakiya domin mutanen dake rayuwa a Saudiyya.
Yanzun mun kara samun wata gagarumar nasara, idan kika je Makka ko Ta'if, Ko Madina, ko Riyad, za ki ga cewa yawan gidajen Talabijin da ke can indai akwai masu magana da hausa, za ki ga an haɗa Manara a ciki. Idan muka je za ki ji suna mana addu'oi suna mana fatan alkhairi, za ki ji sun faɗa ga su kusa da dakin Ka'aba" amma daga Nijeriya suke koyon addini Musulunci.
Bamu tsaya a nan ba, danda muka zauna muka tattauna da ƙungiyar Jaliyat wanda ita ce ƙungiya da ke kula da harkokin addinin Musulunci a Afrika gabaɗaya, kan yaya za a yi da yaranmu dake zaune a wannan kasa waɗanda yawancinsu Hausawa ne 'yan Nijeriya ba su karatu. Ta wace hanya ce za su samu daman yin karatu har zuwa matakin jami'a
Saboda bin sawu da mu ke yi, kungiyar Jaliyat ɗin ta matsawa gwamnatin Saudiyya kuma an kai ga mataki da aka bada dama a buɗe jami'a na irin waɗannan mutane da ke zaune a Saudiyya ba tare da izini ba, wannan jami'ar za'a ba su izini da kuma damar karatu a wannan jami'ar ba tare da an tsagwame su ba. Har mun samu mu yi zaman tattaunawa da su. Gwamntin saudiyya ta ba su izini akai, kuma wannan jami'ar za ta kasance kamar jamai'a ce mai zaman kanta amma sune zasu ringa daukar nauyita.
Shugabannin ƙungiyar Jariyat ɗin irinsu Sheikh Abdul-Razak Al Hausawi, sun taso sun zo Nijeriya mun tattauna da su domin ganin mun haɗa karfi da karfe mun tafiyar da wannan jami'ar. Kuma na san cewa a can Sauddiyar da muka je mun fara tuntubar wasu dattawan Nijeriya dake can da muka san sun damu da al'uma da ilimi da tallafawa, kuma suna da alaƙa da kyau da gwamnatin Saudiyya, kamar irinsu Alhaji Aminu Dantata, mun je mun same shi har gidansa a Jidda mun tattauna da shi, akan yayi amfani da damarsa da alakarsa da sarakuna da masu hali na Saudiyya. A nan ma a Nijeriya da wasu 'yankasu suma sun ba da gudumawarsu don ganin cewa an samar da jami'ar nan da yara za su ci gaba da karatu a ciki.
Abunda ya sa nake ba ki waɗanan dogayen tarihin shine, ko Saudiyya ba su ba da wannan dama na shekara biyu ba, akwai wasu da shakara fiye da goma da ke can, kuma irin matsalolin da ake fuskanta da su a can kenan.
ZT:Matasanmu a yanzun akwai wata al'ada da suka ɗauko, in har an samu saɓanin ra'ayi kan abinda ba su yarda da shi ba, maimakon sukawo hujjojinsu cikin nustuwa yadda za a fahimce amma kawai malam sai ka ji mutum ya danƙaro ashar ko kai tsaye sai la'ana da tsinuwa za su fito bakinsa.
A matsayinka na malami, wace kira ce za ka yi wa Musulninmu game da koyarwar addini kan wannan halin?
Malam Kabiru Gombe:Wannan kuskure babban wadda ka yi haifo da natsaloli da dama cikin al'umma. A Musulunci, hanyar da ka fahimta, sai ka riƙe fahimtarka sannan wani tasa fahimta ta iya saɓawa da taka. Abinda Musulunci ya ce shine ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka kuma ka yi amfani da hikima da wa'azi mai kyau. Abinda aka ɗora maka kenan babu wanda ya ɗora maka la'ana ko tsina masa albarka ba.
Maimakon haka sai ka yi masa addu'ar shiryuwa. Su kuma matasa masu fushi da fushin wani masu zafin kai su sani cewa addinin Musulunci bai yarda da aibata wani ko ka muzguna wa wani saboda kana da saɓanin fahimta ba. Haramu ne ko da kuwa kuskure ya ke yi don ba a gyara kuskure da kuskure.
Na lura irin wannan tunani shiyasa duk lokacin da wani harka ko matsala ta taso za ka fi ganin matasanmu na Arewacin Nijeriya masu danganta kansu da addinin Musulunci su ake samu suna wuce gona da iri har ka ga waɗanda ba musulmi ba waɗanda ba su fahimci addinin Musulunci ba sai ya ɗauka abubbuwan da suke yi shine Musulunci har ya da su su guji musulunci.
To ashe Mudulunci bai ba wa kowa ikon ɗauka doka a hannunsa ba kenan ko Malam? Amma misali, a ce ai ga wannan ko waccan ta zagi Annabi, ya dace mutanen da ke wurin su zartar da hukunci a kansa?
Addinin Musulunci bai yarda mutane su ɗauki doka a hannunsu ba ko da dokar ta Allah ce. Duk wanda ya yi haka ya saɓa wa Allah da Annabi Muhammadu . Ɗauka doka a hannu ya kan kawo fitina a ƙasa.
Hukama ita kaɗai aka yarda su yi hukunci sannan ko hukumar sai ta yi bincike sosai sannan a samu shaidu da sauransu kafin alƙali ya yanke hukunci sannan a zartar da wannan hukunci.
Ba wai kawai da an ce wannan ya zagi Annabi sai a kashe shi, to ko da mutum ya ji ba shi da hurumin ya yanke hunkunci sannan ya zartar da hukuncin a Musulunci. Kai dai naka shaida ne ko ka yi ƙararsa ga hukuma. In misali hukumar ba ta ɗauki mataki ba, babu ruwanka, tsakaninsu da Allah ne, Shi Ya san hanyar da zai yanke hunkuncinSa.
Ba komai ya ke kawo irin wannan ba face jahilci. Indan ba a yi sa'a ba aka samu masu son Musulunci amma ba su da ilimi kan addinin to nan za a samu matsala shiyasa ƙungiyar Izala ta tashi haiƙan don ganin al'umma ta samu ilimi.
source Zuma Times Hausa