An harbe wani dan wasan kwallon kafa a yankin Neja Delta wanda ke buga gasar Firimiyar Nijeriya. Rahotanni sun ce Sojojin da ke fada da tsagerun yankin ne bisa kuskure suka harbe dan wasan mai suna Izu Joseph da ke buga wa kungiyar Shooting Stars wasa.
Wasu rahotanni sun ce an harbe dan wasan ne a wani yankin da sojoji suka kai farmaki kan masu tayar da kayar baya a Niger Delta.
Dan wasan dai ya buga wasan da Shooting Stars ta yi kunnen doki da kungiyar Rangers da ta lashe kofin Firimiya a bana.
Har zuwa yanzu dai a ba ji komai daga rundunar tsaro ba kan kashe dan wasan da suka yi bisa kuskure.
Title :
Sojoji Sun Harbe Wani Dan Kwallo A Yankin Niger Delta Bisa Kuskure
Description : An harbe wani dan wasan kwallon kafa a yankin Neja Delta wanda ke buga gasar Firimiyar Nijeriya. Rahotanni sun ce Sojojin da ke fada da ts...
Rating :
5