Wasu hasallu sun kai farmaki gidan sakataren kungiyar Jama'atu Nasril Islam kuma limamin riko na masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna, Dakta Khalid Abubakar Aliyu, kamar yadda majiyarmu ta Daily Trust ta rawaito.
Lamarin ya auku ne a ranar Juma'ar da ta gabata bayan hatsaniyar da ta kunno kai kan wanda zai ja sallar Juma'a a msallacin na Sultan Bello.
A yayin da yake yi wa majiyarmu ta Daily Trust jawabi, Dakta Khalid ya bayyana cewa sakamakon farmakin da aka kawo gidansa hakan ya sanya iyalansa komawa gidan makwabta.
Ya ce "an kaiwa iyalaina farmaki a ranar Juma'a kuma ina kyuatata zaton Sheik Dakta Ahmed Gumi ne ya turo su. Na godewa Allah babu abinda ya same su har zuwa lokacin da 'yan sanda suka kawo dauki.
"Ba ni na nada kaina a matsayin limamin riko na masallacin ba, kwamitin dake da alhakin nadin karkashin jagorancin Sarkin Musulmi da Sarkin Zazzau ne suka nada ni, kuma ni umarninsu na bi.
Dakta Khalid ya kuma yi kira ga gwamnati da ta shiga lamarin tare da yin kira ga jama'a da su daina daukar doka a hannunsu su dinga bin koyarwar Kur'ani da Hadisi.
A yayin jin ta bakin mai magana da yawun Dakta Ahmed Gumi kuma, Tukur Tanimu ya bayyana cewa "idan Dakta Khalid yana zargin Gumi da turo mutane su kai masa hari gida, sai ha gabatar da shaidu".
Ya kuma kara da cewa Gumi ba shi da wata alaka da wannan hari da aka kai.
A nasa bangaren kuma, kakakin rundunar 'yan sandan jigar Kaduna, ASP Aliyu Usman, ya bayyana cewa kawo yanzu sun kama mutane sha hudu da ake zargin su da neman tada yamutsi a yayin sallar Juma'a a masallacin.
Title :
Sheik Gumi Ne Ya Turo Jama'a Domin Su Kai Farmaki Gidana, - Dr. Khalid
Description : Wasu hasallu sun kai farmaki gidan sakataren kungiyar Jama'atu Nasril Islam kuma limamin riko na masallacin Sultan Bello dake garin Kad...
Rating :
5