Fitaccen Malamin addinin Musulincin nan na Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi kira ga jarumar Kannywood, Rahama Sadau da kada ta amsa gayyatar da wasu fitattun mawaka suka yi mata zuwa Amurka.
Fitaccen mawakin nan Akon da takwaransa Jeta Amata ne dai suka yi gayyaci Rahama Sadau birnin Los Angeles na Amurka domin ta halarci wurin da suke hada sabon fim dinsu na Hollywood.
Sun yi hakan ne, a cewarsu, domin su “karfafa mata gwiwa” bayan korar da aka yi mata da yin fina-finan Kannywood saboda an same ta da laifin rashin da’a sakamakon rungumar da ta yi wa wani mawaki mai suna Classiq a bidiyon wakar da ya sanya ta a ciki.
Sai dai Malam Aminu Daurawa, a wata budaddiyar wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook, wadda kuma ya bukaci a mika sakonsa ga jarumar, ya ce bai kamata jarumar ta amsa gayyatarsu Akon ba, yana mai cewa “Ke dai Musulma ce kuma mu Musulinci shi ne abin dubawa a gare mu.”
Ita dai Rahama Sadau ta ce rungumar da ta yi wa Classiq ba laifi ba ne, tana mai cewa “ba zai yiwu na yi aiki ba tare da na taba wani ba.”
Amma Malam Aminu Daurawa ya ce ya kamata “Ki sani cewa Musulinci addini ne wanda ya yarda da idan mutum ya yi kuskure a kira shi a gaya masa gaskiya, a tunatar da shi ayoyin Allah ko ya gyara.”
Ya bukaci jarumar da ta yi aure domin kuwa shi ne ya fi dacewa da ita.
Title :
Sheik Aminu Daurawa Yayi Kira Ga Rahama Sadau Da kada Ta Amsa Gayyatar Akon
Description : Fitaccen Malamin addinin Musulincin nan na Najeriya, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi kira ga jarumar Kannywood, Rahama Sadau da kada ta a...
Rating :
5