Shugabannin Hadaddiyar kungiyar masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa, wato MOPPAN, ta ce rungumar da Rahama Sadau ta yi wa Classiq, ta sanya mutane suna yi musu kallon mutanen banza.
Shugaban Kungiyar, Muhammad Kabir Maikaba ya shaida wa BBC cewa an dade ana muhawara kan irin hukuncin da ya kamata a dauka a kan ‘yar wasan.
Ya kara da cewa sau uku ke nan Rahama na aikata irin wannan danyen aiki, a inda a wannan karon har sai da aka yi kuri’a kuma masu son a kore ta suka yi rinjaye.
Malam Muhammad ya ce Rahama Sadau da sauran ‘yan mata irinta suna matukar zubar wa kungiyar mutunci a idanun duniya.
Haka ne ya sa kungiyar yanke shawarar korar ‘yar fim din domin ya zamo izna ga masu ra’ayi irin nata.
A ranar Lahadi ne dai kungiyar ta sanar da korar Rahma Sadau bisa rungumar wani mawaki mai suna Classiq a wani faifan bidiyo.
Faifan bidiyon dai ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu sha’awar fina-finan Hausa.
Kungiyar ta MOPPAN dai kuma ta ce an kafa wani kwamiti da zai saurari korafe-korafe da martani game da wannan mataki, musamman daga furodusoshin (masu shirya fina-finan) da a yanzu haka take taka rawa a fina-finansu.
Har yanzu dai jarumar, wacce ke kasar Indiya, ba ta ce komai ba a kan matakin.
bbchausa
Ga Video da ya jawo korar Rahma Sadau https://youtu.be/-n-iyWWBgh4
Title :
Rahma Sadau Ta Zubar Mana Da Kima – MOPPAN
Description : Shugabannin Hadaddiyar kungiyar masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa, wato MOPPAN, ta ce rungumar da Rahama Sadau ta yi wa C...
Rating :
5