Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Rahama Sadau, ta ce ba zai yiwu ta yi aiki ba tare da ta taba wani ba, bayan da aka kore ta saboda rungumar wani mawakin hip hop.
Bayyanar Rahama a wani faifan bidiyo na waka tana rungumar mawaki Classiq ya batawa mutane da dama rai.
Rahama ta ce "Ina neman afuwar wadanda na batawa" sai dai ta ce abin da ta yi din "ba laifi ba ne" a tsarin sana'arta.
Rahama, wacce ke magana a karon farko, tun bayan da kungiyar masu ruwa da tsaki a harkar fim ta Moppan ta kore ta, ta yi yaba wa magoya bayanta kan irin kaunar da suka nuna mata.
Rahama ta bayyana hakan ne a wata sanarwar da ta fitar ranar Talata a shafinta na Twitter.
Ta ce "Na taka rawar da aikina ya bukaci na yi, wanda ko ba a fim din Hausa ba ko da a hakar fina-nan Turanci na Kudancin Najeriya ne [Nollywood] ta kama zan yi hakan. "
Sai dai ta nemi gafarar masoyanta da duk wani wanda abin da ta yi a wakarta da Calssiq ya batawa rai.
Hakazalika ta nemi jama'a su zama masu nuna fahimta ga juna tare da yin watsi da munanan halayen da zai kai ga janyo rabuwar kawuna.
A bara ne Rahama, wacce ta sha jawo cece-kuce a Kannywood, ta fara fitowa a fina-finan Nollywood da ake yi a Kudancin kasar nan.
Sai dai a lokacin ta shaida wa BBC cewa ta fara fitowa a fina-finan Nollywood ne domin ta nuna bajintarta, tana mai cewa ba za ta yi duk wani abu da zai zubar mata da mutunci ba.
Title :
Rahama Sadau Ta Nemi Gafara Kan Rungumar Mawaki Classiq
Description : Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Rahama Sadau, ta ce ba zai yiwu ta yi aiki ba tare da ta taba wani ba, bayan da aka kore ta saboda...
Rating :
5