A daidai lokacin da Najeriya ta ke murnar cika Shekaru 56 da samun ‘Yancin kai daga hannun turawan mulkin mallakar Kasar Birtaniya, wata shahararriyar ‘Yar wasan Nollywood mai suna Cossy Orijiakor, hoto ta dauka a tube domin tunawa da wannan rana mai girma a Najeriya.
Cossy Orijiakor wanda ta shahara wajen wasan kwaikwayo da Nollywood ta saba fitowa a fina-finan Kasar na Nollywood da dama. Cossy Orijiakor ta dauki hoton ta ne a tube, daga ita sai tutar Najeriya inda ta ke taya sauran ‘Yan Kasa da magoya bayan ta murnar wannan rana da Najeriya ta mallaki ‘Yancin Kan ta. Cossy Orijiakor ta aika wannan sako ne tun a Jiya domin murnar bikin Yau.
Yanzu haka dai magoya bayan Tauraruwar ta Nollywood suna ta yada hoton na ta a ko ina. Cossy Orijiakor ta kuma dai yi alkawarin bada kyautar kudi ga wani masoyin ta domin bikin rana ta yau.
A yau ne dai Najeriya ta cika Shekaru 56 daidai da samun ‘Yancin kai daga turawan mallaka na Kasar Ingila. Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari yayi jawabi ga daukacin al’ummar Kasar. Haka nan kuma Tsohon Shugaba, Jonathan Goodluck ya aika da na sa sakon.
Naij Hausa
Title :
Photos: Yar Wasa Nollywood Cossy Orijiakor Tayi Tsirara Dan Bikin Murna 'Yancin Kai Najeriya
Description : A daidai lokacin da Najeriya ta ke murnar cika Shekaru 56 da samun ‘Yancin kai daga hannun turawan mulkin mallakar Kasar Birtaniya, wata sha...
Rating :
5