A yayin sallar Juma'ar yau ne wasu matasa guda uku Allah ya nufe su da shiga Musulunci a Masallacin Juma'a na Karu International Market dake garin Mararrabar Abuja da jihar Nassarawa.
Matasan wadanda suka fito daga sassa daban-daban na kasar nan, bayan sun musulunta an sauya musu suna zuwa Muhammadu, da Abdu'aziz da kuma Hassan.
A yayin jin ta bakin su da wakilinmu ya yi, sun bayyana cewa sun godewa Allah da ya nuna musu wannann ranar, domin Musulunci babbar rahma ce, kuma da yardar Allah ba za su fita daga Musulunci ba har mutuwarsu.
Shi kuma Abdulaziz bayan kammala sallar ya bayyana cewa zai tattara ya koma makarantar Sultan Bello dake Kaduna domin samun ilmin addini.
Title :
Photos: Wasu Matasa Uku Sun Musulunta A Garin Mararraban Gurku
Description : A yayin sallar Juma'ar yau ne wasu matasa guda uku Allah ya nufe su da shiga Musulunci a Masallacin Juma'a na Karu International Ma...
Rating :
5