*Kudinsa Ya Kai Naira Milyan 1.7
Kowane allazi da nashi amanu. Allah ya kawo mu duniya ta zo, kowane zamani na tahowa da irin nashi salon, Karni na 21, wanda aka fi ta’allakawa da karni na ‘yan zamani, na dauke da irin nashi abubuwa da za’a iya lissafa su a cikin cigaban karnin.
Kamfanin “Virgin America” sun kirkiri wani takalmin zamani a karon farko a fadin duniya, takalmi ne da aka yi shi da farar fata, yana dauke da talabijin, wajen cajin wayar hannu, kai har ma da na’urar yanar gizo “Wifi”
A cewar su, sun fitar da wannan takalmin ne a kasuwa, don duk irin kudin da aka samu wajen siyarwa, ayi amfani da su wajen taimakama mabukata. Kimanin kudin takalmin na iya kaiwa dallar Amurka, $4,950 dai-dai da naira milliyan daya da dubu dari bakwai.
Takalmin na dauke da talabijin mai karfin hoton zamani, da mutun zai iya kallon fim, ko wakoki da yake da su a wayar shi ko ya saukar daga yanar gizo. A tabakin daya daga cikin mazanan takalmin, Mr. Mike McKay, suna ganin wanna sabon salon nasu zai samu karbuwa a duniy, domin babu wani kamfani da yataba tunani irin nasu.
Title :
Photos: Takalmi Mai Dauke Da Talabijin, Yanar Gizo Don Matasa
Description : *Kudinsa Ya Kai Naira Milyan 1.7 Kowane allazi da nashi amanu. Allah ya kawo mu duniya ta zo, kowane zamani na tahowa da irin nashi salon,...
Rating :
5