Fitacciyar jarumar finafinan Hausan nan Nafisa Abdullahi ta ziyarci wasu kauyuka a jihar Kaduna inda ta raba musu kayan abinci.
Kauyukan ciki har da kauyen Durguzu, duk suna a yankin karamar hukumar Igabi ne dake jihar Kaduna.
Jarumar wadda ake yi wa lakabi da Nafisa 'Sai Wata Rana' ta yi wannan ziyarar ne tare da abokin aikinta, Abdul M. SHariff inda ya taimaka mata wajen raba kayan abinci, wadanda suka hada da buhunan shinkafa, man gyada, manja, maggi, sabulai da dai sauransu.
Tun kafin zuwan jarumar kauyen, Sarakunan Kauyukan suka taru lsuna jiran isowarta don ganin sun yi mata kyakkyawar tarba.
A yayin jin ta bakin wasu mazauna kauyukan sun nuna farin cikin su tare da bayyana farin cikin su kan ziyarar da ta kawo musu.
Sun kuma kara da cewa sun ji dadi kan yadda ta ziyarce su cikin nishadi da farin ciki baya ga alkairin da ta yi musu.
Title :
Photos: Nafisa Abdullahi Ta Tallafawa Mazauna Wasu Kauyuka Da Kayan Abinci
Description : Fitacciyar jarumar finafinan Hausan nan Nafisa Abdullahi ta ziyarci wasu kauyuka a jihar Kaduna inda ta raba musu kayan abinci. Kauyukan c...
Rating :
5