Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani mai gadin makabarta mai suna Oluwatosin Akorede, saboda samun sa da kokon kawunan mutane har guda biyu.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Mista Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan a garin Abeokuta babban birnin jihar.
Mista Abimbola ya ce an kama Oluwatosin ne da misalin karfe bakwai na dare a garin Isale-Iko dake karamar hukumar Sagamu bayan sun bi sahun shi.
Rundunar tace ana nan ana gudunar da bincike domin sanin dalilin da ya sa shi aikata wannan danyen aikin.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu tuni ya bayar da umurnin kai wanda aka kaman sashin kula da manyan laifufuka na rundunar dake Eleweran a garin Abeokuta.
Title :
Photos: An Kama Wani Mai Gadin Makabarta Da Kokon Kawunan Mutane Biyu
Description : Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani mai gadin makabarta mai suna Oluwatosin Akorede, saboda samun sa da kokon kawunan mutane har g...
Rating :
5