'Yar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Fatima na shirin auren tsohon manajan-darakta na bankin Mortgage, Malam Gimba Ya'u Kumo.
Za a yi bikin ne a ranar Juma’a mai zuwa (28 ga watan Oktoba) a jihar Katsina.
Fatima ta kasance yarinyar shugaban kasa Buhari ta biyu daga matar sa ta farko Safinatu Muhammadu Buhari.
Shugaba Buhari ya auri tsohuwar matarsa, marigayiya Safinatu Muhammadu Buhari a shekara ta 1971 tana da shekaru 18 da haihuwa, an haife ta a ranar 11 ga watan Disamba ta shekarar 1952, a cikin zuri’ar Fulani kuma tana da nasaba da Shehu Usman Danfodio.
Sun samu yara biyar da juna, Zulaiha (Marigayiya), Fatima, Musa, Hadiza da kuma Safinatu Buhari.
Madogara Rariya
Title :
Photos: Buhari Zai Aurar Da 'Yarsa, Fatima
Description : 'Yar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Fatima na shirin auren tsohon manajan-darakta na bankin Mortgage, Malam Gimba Ya...
Rating :
5